Vieira; Akwai Bukatar Kara Zage Dantse Domin Yaki da Wariyar Launin Fata.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace Patrick Vieira, ya bayyana cewa akwai bukatar a kara tashi tsaye wurin kawar da nuna wariyar launin fata da ake yi wa ‘yan wasa a gasar ta firimiya.
Viera yana martani ne bayan da aka fitar da sanarwar cewa za’a rage dabi’ar saka gwiwa daya a kasa gabanin fara wasannin kakar bana, wata alama da ke nuna adawa da nuna wariya ta fara zuwa karshe.
An takaita hakan in ban da a manyan wasannin gasar Premier League da kuma wasannin karshe na kofin FA da kuma Carabao sai dai tsohon kyaftin din na Arsenal kuma mai horar da Crystal Palace Patrick Vieira ya ce ana wasa da muhimmancin da adawa da nuna wariyar ke da shi, domin a cewarsa abu ne da ya kamata a karfafa yi a maimakon yi masa rikon sakainar kashi ba
Yana da muhimmanci a ci gaba da saka kafa a kasa domin nuna adawa da nuna wariya don duk muna adawa da hakan kuma yaki ne da zai dauki tsawon lokaci ana yi a don haka dole mu ci gaba da saka gwuiwa a kasa,” in ji Vieira.
A watan Fabrairun shekara ta 2021 ne dan wasan gaban Crystal Palace Wilfried Zaha ya daina dabi’ar saka gwiwa a kasa, inda ya kafa hujja da cewa yin hakan bai sauya komai ba domin har yanzu da dama daga cikinsu na fuskantar wariyar launin fata.