Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA)ya ce Isra’ila ta kai hari kan ɗaya daga cikin makarantunta a Gaza “ba tare da yin gargaɗi ba” ga dubban masu neman mafaka a wajen.
“Wata mummunar ranar a Gaza,” kamar yadda Philippe Lazzarini ya rubuta a shafinsa na X.
“A wannan karon a Nuseirat, a yankin tsakiya, Sojojin Isra’ila sun afka cikin dare ba tare da gargadin farko ga ‘yan gudun hijirar ko UNRWA ba,” in ji shi.
“An sake kai hari kan wata makaranta ta UNRWA da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka,” in ji Lazzarini.
Yawan Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kai 36,654 — Ma’aikatar Lafiya
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce aƙalla mutum 36,654 ne aka kashe a cikin kusan wata takwas na yaƙin da Isra’ila take yi a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Wata sanarwar ma’aikatar ta ce hakan ya haɗa har da mutum 68 da aka kashe cikin awa 24, inda ta ƙara da cewa an kuma jikkata mutum 83,309 a Gaza tun fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Hukumar MDD ta yi gargaɗin cewa annobar kwalara za ta ɓarke a Gaza yayin da ake fama da tsananin rashin ruwa
Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu ta Majakisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi gargaɗin cewa za a samu ɓarkewar annobar amai da gudawa a Gaza a yayin da ake fama da matsanancin ƙarancin ruwa sakamakon hare-haren Isra’ila.
A sanarwar da ta fitar, UNRWA ta ƙara da cewa “A yayin da ake ci gaba da fama da tsananin rashin tsabtataccen ruwan sha da kuma tsananin zafi a Zirin Gaza, akwai barazanar ɓarkewar cututtuka da motsewar jiki saboda rashin ruwan sha.”
DUBA NAN: Sakon Jagora A Iran Ga Matasan Amurka
“Akwai damuwa sosai cewa kwalara na iya ɓarkewam lamarin da ka ita ta’azzara mummunan yanayin da mutane ke fama da shi.”