UNRWA: Babu wani amintaccen guri a Gaza, har ma da matsugunai na Majalisar Dinkin Duniya
Hukumar Ba da Agaji da Samar da ayyukan yi ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira ta sanar da cewa, Isra’ila ta kaiwa makarantu da ma’aikatu 84 hari na kai tsaye a cikin kisan kare dangin ta keyi a zirin Gaza, wanda hakan ya janyo cewa Babu wani amintaccen a Zirin Gaza.
Hukumar Ba da Agaji da Samar da Aikin yi ga Falasdinawa ‘Yan Gudun Hijira a Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta sanar da cewa tun daga farkon yakin Gaza, akalla makarantu 84 da ke da alaka da wannan kungiya ta kasa da kasa ke fuskantar hare-haren Isra’ila kai tsaye tare da lalata su.
Hukumar ta kuma sanar da cewa sama da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa miliyan 1.7 ne ke matsuguni a ciki ko kusa da wuraren har zuwa ranar Asabar din da ta gabata.
Kuma ta sanar dacewa Akalla mutane 400 ne suka rasa matsugunansu a wannan wurin ko kuma a kusa da shi a lokacin hare-haren Isra’ila kuma sama da mutane 1300 suka jikkata.
” Babu wani amintaccen guri a Gaza da ke da tsaro, hatta matsugunin Majalisar Dinkin Duniya,” UNRWA ta rubuta a cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na sada zumunta na X.
A ranar Talata ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da karuwar adadin shahidan zuwa 29,878 sannan adadin wadanda suka jikkata zuwa 70,215.