Zalika wasan kofin na Carabao shi ne nasarar da West Ham ta samu kan United a filin wasa na Old Trafford a karon farko tun shekarar 2007.
A sauran wasannin da aka kara, Chelsea da Tottenham sun tsallake rijiya da bayan a matakan bugun fanareti, inda suka samu nasarar tsallakawa zagaye a gasar kofin na Caraboa.
A wasan da aka kara tsakanin Chelsea da Aston Villa an tashi 1-1, a bugun fanareti kuma Chelsea ta yi nasara da 4-3, yayin da Tottenham ta doke Wolves da 3-2 a bugun na daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka tashi 2-2 a wasan da suka fafata.
A wani labarin na daban rahotanni daga Ingila na cewa shugabannin kungiyar Manchester United sun fara nazari kan mutane 3 da suka cancanci maye gurbin kocinsu na yanzu Ole Gunnar Solskjaer.
Magoya bayan United da kuma wasu masu sharhi kan kwallon kafa, sun caccaki matakin da Solskjaer ya dauka yayin wasan, inda ya maye gurbin Jadon Sancho da Diogo Dalot, bayan da aka kori Aaron Wan-Bissaka saboda jan kati.
Sai kuma cire Cristiano Ronaldo da Bruno Fernandes da yayi, yayin da ya rage saura mintuna 20 a tashi, lokacin da wasa ke 1-1.
A halin yanzu United ta yi rashin nasara a wasanni 7 daga cikin 11 na gasar Zakarun Turai a karkashin Solskjaer, abinda ya sanya wasu fara kiraye -kirayen neman a sallame shi.
Rahotanni kamar yadda jaridar UK Mirrow ta ruwaito na cewa, ana sa ran United ta tantance wanda za ta kulla yarjejeniya da shi, tsakanin Antonio Conte, Zinedine Zidane da Brendan Rodgers.
Conte da Zidane dai a yanzu haka babu wata kungiya da suke horaswa, bayan rabuwa da Inter Milan da Real Madrid, yayin da Rodgers ke jagorantar Leicester City.