KAI-TSAYE: Yara 940 sun bace a Gaza: UNICEF
KAI-TSAYE: Yara 940 sun bace a Gaza: UNICEF
Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra’ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kananan yara da mata ne aka fi kashewa a Gaza a wannan rikici, kamar yadda alkaluma suka nuna. Hoto/Reuters
1127 GMT — An kashe Falasdinawa 8,525 a Gaza zuwa yanzu
Akalla Falasdinawa 8,525 daga ciki har da yara 3,542 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda ma’aikatar lafiya da ke Gaza ta bayyana a ranar Talata.
Ma’aikatar ta ce an kashe ma’aikatan lafiya 130 sannan akwai asibitoci 15 wadanda suka rufe.
1030 GMT — Yara 940 sun bace a Gaza: UNICEF
Asusun Kula Da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa akwai akalla yara 940 a Gaza wadanda suka bace babu labarinsu.
Haka kuma asusun ya yi gargadi kan cewa Gaza na neman zama makabarta ga yara kanana a halin yanzu.
Asusun ya ce ana kara samun adadin yaran da ke mutuwa a kullum a Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa
1000GMT — Jami’an diflomasiyyar Qatar da Amurka sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza
Ministan Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya tattauna da takwaransa na Amurka Antony Blinken kan hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kai wa a Gaza.
Blinken ya kira Al Thani, wanda kuma shi ne firaiministan, ta wayar tarho inda “suka tattauna kan yadda lamura ke ta’azza a Gaza da kuma bukatar tsagaita wuta nan-take,” a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta fitar.
Kazalika sun tattauna kan matakan baya-bayan nan game da sulhu domin sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
0800 GMT — Isra’ila ta kashe Falasdinawa 15 a harin da ta kai wani gida a tsakiyar Gaza
Aƙalla Falasɗinawa 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai wani gida na zuri’ar Abu Shamala a unguwar Zawaida da ke yankin tsakiyar Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya bayyana, yana mai ambato majiyyin watsa labarai.
WAFA ya ce jiragen yaƙi sun kuma kai hari wani gini mai hawa huɗu a unguwar Zaytounda ke kudu maso gabashin Gaza, inda gwamman mutane suka jikkata.
Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren sama babu ƙaƙƙautawa a dukkan yankunan Gaza, lamarin da ke ta jawo mace-mace da jikkata Falasɗinawa.
0750 GMT — UNRWA tana makokin ma’aikatanta 63 da aka kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba
Hukumar Ayyuka da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi makokin ma’aikatanta 63 da aka kashe a Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa tun daga 7 ga watan Oktoba.
“Babu wata kalma da za ta fayyace irin baƙin cikin da muke ciki na kashe ma’aikatanmu na UNRWA 63 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba,” kamar yadda UNRWA ta wallafa a shafinta na X.
“Dole ne a yanzu a kawo ƙarshen wannan kashe-kashe da wahalhalun da ake sha a kullum,” hukumar ta ƙara da cewa.
Ta ce duk da dumbin barazanar da ma’aikatanta ke fuskanta, UNRWA za ta ci gaba da yi wa mutanen da ke cikin buƙata hidima a Gaza.
UNRWA ita ce babbar hukumar MDD da ke aiki a Gaza.
Source: TRT Hausa