Ukraine;matsayin manyan ƙasashen duniya a kan farmakin Rasha?
Manyan ƙasashen duniya kamar su Amurka da Birtaniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai sun fito gaba-gaɗi sun yi Allah-wadai da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.
Sun kuma jagoranci ƙoƙarin ƙaƙaba wa Rasha takunkumai tare da aika wa Ukraine agajin kayayyakin yaƙi.
Sai dai martanin da ake ta mayarwa a kan Rasha ya sha bamban a tsakanin ƙasashen duniya.
A wannan maƙalar, mun yi duba kan matsayar manyan ƙasashen duniya da kuma abin da shugabanninsu suka ce kan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.
China
Babban abin lura a kan martanin China kan yaƙin shi ne rashin jin ta bakin Shugaba Xi Jinping – a maimakon haka, sai sakataren harkokin wajen ƙasar ne yake ta fitar da sanarwa.
A sanarwarsu ta ranar 25 ga watan Fabrairu, Beijing ta ce ta amince da “ƴanci da kiyaye iyakokin dukkan ƙasashen”, sannan ta bayyana cewa Rasha tana da “ƙwararan dalilan nuna damuwa ga tsaronta” wanda ya kamata a ɗauka da muhimmanci a kuma duba matsalar.”
Sai dai har zuwa yanzu China ba ta yi amfani da kalmar “kutse ba” – a kan batun matakin da Rasha ta ɗauka a Ukraine ba.
Ƙwararrun masu sharhi kan diflomasiyya ba su yi mamakin matsayar ba har ma suka ce ai ko ranar 4 ga watan Fabrairu shugaban China Xi da na Rasha Vladimir Putin sun gana a Beijin – haɗuwarsu ta 38 kenan tun shekarar 2013.
Dukkan shugabannin sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka yi kira ga ƙasashen Yammacin Duniya da su yi watsi da “aƙidojin da suke bi na yaƙin cacar-baka.”
Abin da ya fi fitowa fili sosai shi ne China ta ƙi kaɗa ƙuri’a a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don watsi da kutsen Rasha.
Indiya
Awanni bayan da Rasha ta kutsa Ukraine sai ga saƙo daga Indiya ta bakin ƙaramin Ministan Harkokin Cikin Gidanta, Rajkumar Ranjan Singh, yana cewa ƙasar ‘yar ba-ruwana ce a wannan matsala.
Sannan ƙasar ta ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan kutsen.
Rasha da Indiya sun daɗe da ƙulla alaƙa kan harkokin tsaro, amma Firaministan Indiya Narendra Modi yana tuntuɓar shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
A ranar 26 ga Fabrairu ne Firaminista Modi ya buƙaci “ba da gudunmawarsa ta kowace hanya kan ƙoƙarin samar da zaman lafiya”, a cewar mai magana da yawun gwamnatin.
Turkiyya
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ba za ta iya yasar da alaƙarta da Rasha ko Ukraine ba, yana mai ƙarawa da cewa Ankara za ta wanzar da yarjejeniya kan mashigar tekunta don hana rikicin yin ƙamari.
Kafar yaɗa labaran Turkiyya ta ruwaito cewa ƙasar ta yarda ta haramta wa jiragen ruwan yaƙi wucewa ta Baharul Aswad wato Black Sea ta mashigar ruwan Turkiyya.
Turkiyya, wadda mamba ce a ƙungiyar tsaro ta Nato, ta yi iyaka da Ukraine da Rasha a Baharul Aswad kuma tana da kyakkyawar alaƙa da kowaccensu. Ukraine ce ta buƙaci a rufe mashigun na Turkiyya.
Turkiyya ta mayar da martani da kakkausar sanarwa kan kutsen da Rasha ta yi, tana mai bayyana matakin sojin da “rashin adalci da kuma keta doka”, inda ta ƙara da cewa rikicin “yana yin barazana sosai ga tsaron yankinmu da duniya baki ɗaya”.
“Mun yi tur da matakin sojin da Rasha ta ɗauka,” a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a wani jawabin da ya yi a talabijin a makon da ya gabata.
Erdogan ya ziyarci Ukraine a farkon watan Fabrairu ya kuma mayar da ganawar wajen sa baki a daidaita rikicin Kyiv da Moscow.
Sannan an ƙulla yarjejeniyar da za ta bai wa ƴan Ukraine damar ƙera jirage marasa matuƙa na Turkiyya waɗanda tuni aka kai su yankin Donbas don yaƙi da ƴan tawayen da Rasha ke goyon baya.
Iran
Ra’ayin Iran kashi biyu ne: wasu jami’an gwamnatin ƙasar sun bayyana cewa suna tur da yaƙin, duk da cewa wani sashen na Tehran na ganin ƙasashen Yamma ne suka assasa rikicin.
Shugaba Ebrahim Raisi ya shaida wa Vladimir Putin a wajen wani taro ranar 24 ga Fabrairu cewa: “Faɗaɗa ayyukan Nato babbar barazana ce ga tsaron ƙasashe masu ƴancin kai a yankuna daban-daban.”
Ministan Harkokin Waje, Hossein Amir-Abdollahian, ya wallafa sako a Tuwita cewa rikicin Ukraine ya samo asali ne saboda batun “faɗaɗa ikon Nato”, amma ya kuma rubuta cewa “ba mu yarda cewa yaƙi ne zai warware wannan taƙaddama ba”.
Myanmar
A ganin gwamnatin soji a Myanmar kuwa, “babu dalilin yin” kutsen na Rasha, ta kuma bayyana matsayin Rasha a matsayin ƙasa mai ƙarfin faɗa-a-ji ta duniya, kamar yadda mai magana da yawun sojin ƙasar Janar Zaw Min Tun ya ce a wata sanarwa da ya fitar.
Rasha dai babbar ƙawa ce ga Myanmar kuma mai ba ta makamai kamar China.
Brazil
Shugabannin manyan ƙasashen Latin Amurka sun soki Rasha kan wannan kutse a Ukraine, amma shirun da Brazil ta yi kan batun yana ba da mamaki.
Shugaba Jair Bolsonaro, wanda a kwanan baya ya gana da takwaransa na Rasha a Moscow, bai ce komai ba kan ɗaukar wasu matakai a kan ƴan ƙasar da suka maƙale a Ukraine.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Brazil ta yi kira a dakatar da rikicin sannan ta ce a warware shi ta hanyar diflomasiyya. Haka kuma, ta bayyana kutsen a matsayin “cinye iyakokin Ukraine ta hanyar amfani da ƙarfin soja”.
Babbar ƙasar ta yankin Latin Amurka ta kuma ƙi goyon bayan sanarwar haɗin gwiwa ta Ƙungiyar Ƙasashen Amurka da ta yi Allah-wadai da kutsen Rasha a Ukraine, wanda dukkannin ƙasashen yankin suka mara wa baya.
Sannan Brazil ta kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da kutsen Rasha a Ukraine a wajen taron Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ƙasashen Afirca
Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU, mai ƙasashe 55 a nahiyar ta yi kira ga Rasha da ta girmama dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ƴancin Ukraine a wata sanarwa da ta fitar ranar 24 ga watan Fabrairu.
Shugaban AU Macky Sall da kuma Moussa Faki duk sun roƙi Moscow da Kyiv da su “tsagaita wuta tare da fara tattaunawar dimokraɗiyya don kare duniya daga afkawa bala’in yaƙi”.
Amma martani mafi jan hankali daga wani ɗan Afirka ya fito ne daga bakin jakadan Kenya a Majalisar Dinkin Duniya, Martin Kimani, yayin wani jawabi.
Kimani ya gabatar da jawabi mai ƙarfi ga taron Kwamitin Tsaro kwana uku kafin kutsen inda ya alaƙanta goyon bayan da Rasha take nuna wa ƴan a-ware da irin yanayin mulkin mallakar da aka yi wa Afirka a baya.
“Iyakokin ba waɗanda muka tsara wa kanmu ba ne. An tsara su ne a zamanin mulkin mallaka a London da Paris da Lisbon, ba tare da la’akari da tsofaffin ƙasashe masu tarihi da suka rarraba ba,” in ji shi.
Kudu maso gabashin Asia
Kungiyar kasashen kudu maso yammacin Asiya (ASEAN) mai mambobi 10 da suka hada da Myanmar sun fitar da wata sanarwa ranar 27 ga watan Fabrairu da ta kauce wa ambato Rasha ko yin tir da mamayar.
Cikin martanin da kasashen suka fitar daya bayan daya, Singapore ce ta fi yin suka mai karfi, inda ta ce “ba ma goyon bayan dukkan wata mamaya da wata kasa ke yi wa wata kasar ko ma mene ne dalilin yin haka.”
Indonesia ta ce ba ta “amince da matakin sojin da aka dauka ba”, sai dai ba ta ambaci Rasha ba.
A Philippines kuwa, Sakataren Tsaro na kasar Delfin Lorenzo a ranar 26 ga Fabrairu ya ce matsayar kasar “na ‘yan ba ruwanmu ne.”
A watan Yunin bara, Shugaba Rodrigo Duterte ya sanar cewa Philippines za ta bunkasa kawancenta da Rasha a wasu fannoni ciki har da na tsaro.
America
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Rasha ta yi wannan mamayar ne kawai ba tare da an takale ta ba, kuma ba tare da wata hujja ba.
Shugaba Biden ya ce “Putin ne ya zabi yin wannan yakin, kuma shi da kasarsa za su dandana kudarsu.”
Baya ga kakaba wa Rasha sabbin takunkumai, Biden ya kuma ce zai aika da dakarun kasarsa zuwa kasashen Turai.
Sai dai shugaban ya ce sojojin Amurka ba za su kara da na Rasha ba kai-tsaye a rikicin na Ukraine.
Birtaniya
Yayin wata ziyara da ya kai Poland ranar 1 ga watan Fabrairu, Firaminista Boris Johnson ya ce Vladimir Putin na daukar matakai “na mutanen da ba su waye ba” a rikicin na Ukraine.
Birtaniya ta dauki matakan ladabtarwa kan Rasha kuma tana duba yiwuwar a kore ta daga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Tarayyar Turai
Baya ga yin tir da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, Tarayyar Turai ta yi kira ga mambobin kungiyar da su dauki matakan ladabtarwa kan attajiran Rasha da makusantan shugaban kasar. Ta kuma bukaci da su daina sayen iskar gas da man fetur daga Rasha.
Sai dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ranar 1 ga watan Maris ya bukaci Tarayyar Turai ta “tabbatar mana cewa kuna tare da mu”, kana daya bayan da ya nemi Tarayyar ta shigar da kasarsa cikin kungiyar.