Ukraine ta zargi Rasha da sace mata kayan abinci.
Mataimakin ministan noma na Ukraine ya zargi Rasha da sace wa Ukraine ton 100,000 na kayan abinci yankunan da dakarunta suka mamaye.
Taras Vysotskiy ya ce yana fargabar cewa Rasha za su iya wawushe shaguna ton miliyan daya da rabi na amfanin gona.
Ukraine ta ce kwasar ganimar kayan abinci da kuma toshe hada-hadar jirage a tashoshin ruwanta na iya yin barazana ga samar da abinci a duniya.
Kakakin Kremlin ya musanta zargin na satar abinci.
RAED MORE : Ramadan; Yadda Musulmai a Birtaniya suka yi azumi a cikin ƙunci.
Wannan na zuwa yayin da jirgin farko da ke cike da kayan abinci na Ukraine ya bar tashar ruwan Romania a ranar Juma’a, wanda ya ba Ukraine damar kaucewa takunkumin Rasha.
READ MORE : Quds; Yahudawan Sahyuniya Sun Auka Kan Masallata A Masallacin Al-aqsa.
READ MORE : Jagora; Kowace Rana ranar Quds Ce Matukar Dai Yahudawa Suna Mamaye Da Masallacin Al-aqsa.