Ukraine na buƙatar ƙarin Gas da makamai – Zelensky
Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya umarci ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ta G7 da su samar wa ƙasarsa ƙarin gas da makamai domin taimaka mata kuɓuta daga matsanancin sanyin da ke yin barazana ga rayuwar miliyoyin al’umar ƙasar da ke fama da hare-haren Rasha.
Sakamakon dusar ƙanƙara da ke ci gaba da sauka a wasu sassan ƙasar da kuma lalala tashar wutar lantarkin ƙasar da Rasha ta yi, mafi yawan al’umar ƙasar na fama matsanancin sanyi sakamakon rashin makamashin da za su ɗumama jikinsu da shi.
Yayin da yake jawabi ga taron ƙungiyar ta G7 ta bidiyo ranar Litinin, shugaba Zelensky ya ce Ukraine na buƙatar ”kusan cubic miliyan biyu” na gas a wannan lokacin na hunturu.
Ya kuma buƙaci ƙasashen da su aika wa Ukraine da ƙarin makamai ciki har da tankokin yaƙi da makaman atilari da makamai masu cin dogon zango.
Read More :
Mazauna Amurka da Kanada na bikin Kirsimeti ba lantarki, cikin bala’in sanyi.
Qassem Soleimani ya gina dakaru fiye da na Amurka!
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori jami’anta bakwai a jihar Imo.