Ukrain; An Yake Wa Yan Burtaniya 2 Da Morocco Guda Hukuncin Kisa.
Mayaka masu goyon bayan kasar Rasha a Ukrain sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya da wani guda dan kasasar Morocco wadanda suke yaki a bangaren Ukrain, kuma an yanke masu hukuncin kissa a wani kotun soje a lardin Donetsk
Kamfanin dillancin labaran reuters ya kara da cewa Kotun ta sami yan kasar ta Burtaniya masu suna Aiden Aslin da kuma Shaun Pinner, da kuma dan kasar Morocca mai suna Brahim Saadoun da laifin kokarin kifar da halattaciyar gwamnatin a yankin.
Labarin ya kara da cewa mutanen 3 an kama su ne bayan da kasar Rasha ta fara aikin soje na musamman a kasar Ukrai, a ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata. Amma lawyansu y ace suna iya daukaka kara.
READ MORE : Morocco Ta Haramta Nuna Fim “The Lady of Heaven” A Kasar.
Gwamnatin kasar Burtaniya dai ta yi allawadai da hukuncin, kuma ta kara da cewa abin kunya ne yin hakan. Sannan firai ministan kasar Boris Jonson ya ce ai an kama su ne a matsayin fursinonin yaki, sannan akwai dokokin Geneva da suka yi magana kan matsayin fursinonin yaki ba wai a kaisu kotu ba.