UAE Wani Kwamandan Sojojin Amurka Ya Isa Abudhabi Don Taimaka Mata Kan Yemen.
Babban kwamandan rundunar sojojin Amurka a yammacin Asia Janar Frank McKenzie ya isa birnin Abudhabi a jiya Lahadi, don taimakawa gwamnatin kasar wacce makamai masu linzami na sojojin kasar Yemen suka rikata al-amuranta a cikin watan da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami da wasu jiragen da ake sarrafasu daga nesa kuma masu konan bakin wake kan wasu wurare masu muhimmanci a Dubai da Abudhabi na UAE har sau uku a cikin watan Jenerun da ya gabata.
Gwamnatin kasar UAE ta kasa kare kanta daga wadannan hare-haren maida maratani wadanda sojojin kasar Yemen suka yi, don haka ne ta bukaci taimakon Amurka don yin hakan.
Janar McKenzie ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kafin ya isa Abudhabi kan cewa : Lalle suna cikin damuwa sosai kuma suna bukatar taimako, don haka ne mu ka ga yakamata mu taimakamasu, kuma zamu bada taimakon da suke nema.
Kasar Saudiya da UAE ne suke jagorantar yakin shekaru 7 kan kasar Yemen da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar, amma nasarar da sojojin Yemen suka samu a kansu ya nuna cewa suna nesa da cimma manufarsu.