Tunsia Alkalai A Kasar Sun Zargin Shugaba Sa’id Da Neman Ikon Da Bai Da Iyaka.
Alkalai a kasar Tunisia sun nuna rashin amincewarsu da shirin shugaba Kais Saeedna rusa majalisar koli ta alkalan kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa majalisar alkalan ita ce kadai da rage wacce zata iya takawa shugaban kasar biriki a shirinsa na sauya tsarin shugabanci a kasar.
Alkalan sun zargi shugaban da son mulki, sannan suna ganin rusa majalisar koli ta alkalan kamar kwace ‘yencin da bangaren shara’a yake da shi a kasar.
Kafin haka dai shugaban ya kori Frai ministan kasar ya rufe majalisar dokokin kasar sannan ya sannan ya ce zai shugabanci kasar kirkirannun dokoki sannan zai sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar na shekara ta 2014 kafin ya nemi jin ra’yin jama’ar kasar a wani zaben raba gardaman da zai gudanar. Mafi yawan yan siyasar kasar dai suna ganin yayi masu juyin mulki ne.