Tunisia ; Zanga zangar Kin Jinin Shugaba Kais Saied, Na Dada Kamari.
A Tunusia, dubban mutane ne suka gudanar da wata zanga zanga ta nuna kin jinin shugaban kasar Kais Saied.
Zanga zangar wacce akasarin wadanda sukayi ta ‘yan jam’iyyar islama ta Ennahdha ne, na kira ga shugaban kasar ya sauka daga kan mulki.
An dai zuba jami’an da na kwantarda tarzoma da dama gabanin zanga zangar ta jiya Lahadi.
A Tunusia, tun dai bayan da shugaban kasar ya rusa majalisar dokoki bangarori da dama a kasar ke zarginsa da juyin mulki.
READ MORE : ‘Yan Polisario Sun Soke Duk Wata Alaka Ta Tuntuba Da Spain.
A ranar 30 ga watan Maris da ya gabata ne, Shugaba Kais Saied, ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar lamarin da bangarorin ke cewa babu demokuradiyya idan ba bangaren majalisa.
Ko baya ga rikicin siyasa kasar ta Tunusia, na fama da matsin tattalin arziki.