Tunisia; Jam’iyyar Ennahda Ta Ce An Daukewa Wani Jigon Jam’iyyar Daurin Talala.
a masu kishin addini a kasar Tunisia ta bada sanarwan cewa an daukewa Nuruddeen Bhairi daurin talalan da aka yi masa a jiya da yamma.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar jam’iyyar tana fadar haka a shafinta na twitter. Har’ila yau ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar ta Tunisia ta tabbatar da wannan labarin.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Kais Said ta yiwa Bhairi daurin talala ne a cikin watan Dicemban da ya gabata, saboda zargin cinhanci da rashawa. Banda Bhairi dai akwai wasu ‘yan siyasa da dama da suke tsare ko kuma wadanda suke cikin daurin talala tare da Umurnin shugaba Sa’id.
A cikin watan Yulin da ya gabata ne shugaban ya kori majalisar dokokin kasar ya kuma kori firai ministan da ministocinsa. Sannan ya fara gabatar da sauye-sauyen a harkokinn gudanarwan kasar.