Thomas Tuchel ya ce Chelsea za ta ci gaba da kasancewa kungiyar kwallon kafa mai karfi duk da sanarwa mai ratsa zuciya da mai kungiyar, Roman Abramovich ya bayar na cewa zai sayar da kungiyar, sakamakon mamayar Ukraine da Rasha ta yi.
Sanarwar tasa ta zo ne gabanin wasan cin kofin FA na tsakiyar mako da Chelsea ta doke Luton 3-2.
Tuchel ya ce mai bada shawara kan tsare-tsare da ci gaba a kungiyar, Petr Cech ya yi wa ‘yan wasa da ma’aikatan kungiyar bayani a kan al’amarin.
Ya ce babu wani abin damuwa a kan wannan batu, duba da cewa Chelsea ta riga ta kawo karfi gabagadi, kuma babu abin da zai jijjiga ta, ko da yake ‘yan wasan sun shiga wani hali na damuwa bayan sanarwa.
A wani labarin na daban Attajirin kasar Rasha Roman Abramovich, ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar sayar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, shekaru 19 bayan mallakarta.
Attajirin ya kuma yi alkawarin bayar da gudummawar kudi daga cinikin saida kungiyar ta Chelsea da za a yi domin taimakawa wadanda yakin Ukraine ya shafa.
Abramovich mai shekaru 55 da haihuwa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sayar Chelsea shi ne mataki mafi dacewa da zai amfani kungiyar mai rike da kofin gasar zakarun Turai.
Wannan kuwa nada nasaba da mamayar da Rasha ta yi Ukraine, yayin da ake kallon Abramovich a matsayin daya daga cikin na hannun daman shuganan Rasha Vladimir Putin.
Attajirin na Rasha ya kara da cewar, ba zai nemi kungiyar ta biya shi bashin da ya bata na fam biliyan 1.5 kwatankwacin dala biliyan 2.
Tun daga karshen makon jiya ne dai makomar Roman Abramovich a matsayin mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ke cikin barazana bayan wani attajirin Swizerland ya yi ikirarin cewa, tuni aka yi masa tayin sayen kungiyar ta Chelsea.
Biloniyan attaijirin mai suna Hansjorg Wyss ya shaida wa Jaridar Blick cewa, Abramovich na son raba gari da Chelsea cikin gaggawa bayan yin barazanar lafta masa jerin takunkumai a majalisar dokokin Ingila.
Tuni ma dai Abramovich din ya mika ragamar kungiyar ta Chelsea ga wasu mambobin kwamitin amintattu na kungiyar domin ci gaba da kula da ita.