Tsohon Shugaban Burkina Blaise Compaoré Zai Koma Gida.
Bayanai daga Burkina faso na cewa, tsohon shugaban kasar Blaise Compaoré, zai koma kasar a cikin kwanaki masu zuwa, bayan gudun hijira da ya ke a Ivory Coast tun cikin shekarar 2014 bayan hambarar da mulkinsa.
Rahotanni sun ce ana sa ran tsohon shugaban zai gana da shugaban mulkin rikon kwaryar soji na kasar Laftana Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba.
Majiyoyin da dama sun ce wannan na daga cikin fatan shugaba Damiba, na ganawa da tsohon shugaban kasar a yunkurin da yake na hada kan ‘yan kasar.
Saidia ba’a bayyana lokaci ba ko ranar takamaimai da za’ayi wannan ganawar ko kuma wacce tsohon shugaban Blaise Compaoure zai koma kasar.
READ MORE : Aljeriya Ta Yi Wa Fursunoni 14,000 Ahuwa Albarkacin Ranar ‘Yanci.
Dama dai a kwanan baya shugaban mulkin sojin kasar ya gana da wasu tsaffin shugabanin kasar da suka hada da Jean Baptiste Ouédraogo da Marc Rock Christian Kabore da sojojin suka kwace mulki hannunsa.
READ MORE : ‘Yan Siyasa A Sudan Sun Yi Fatali Da Tayin Janar Al-Burhan.
READ MORE : Amurka; Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 6 Yayin Faretin Ranar ‘Yancin Kai.
READ MORE : AU Ta Yaba Da Samun Ci Gaban Siyasa A Mali Da Guinea.