A karon farko tsohon jagoran ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ake zargi da aikata laifukan yaki da kuma ta ke hakkin bil-Adama Maxime Makom, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Makom mai shekaru 43, a ranar Litinin ne Chadi ta mika shi ga hukumomin kotun ta ICC da ke birnin Hague a Holland, inda ya tabbatar da cewar an shaida masa lafukan da ake zargin sa da aikatawa.
Lauyan sa ya bayyana cewar, hukumomin Chadi sun azabtar da Makom a tsawon lokacin da ya shafe a hannunsu ta yadda suka rika ciyar da shi lalataccen burodi baya ga barinsa ya kwana a kasa ba gado.
An dai tsaida ranar 31 ga watan Janairun badi domin fara sauraron karar.
Rikicin da ‘yan tawayen Seleka da kuma Balaka suka haifar a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma sanya wasu rasa muhallan su.
Tuni dai aka gurfanar da biyu daga cikin wadanda suka jagoranci tawaye a kasar, Patrice Edouard Ngaissona da kuma Alfred Yekatom a gaban kotun, yayinda aka tsaida watan Satumba don fara shari’ar Mahamat Said Abdel Kani wanda ake zargi a matsayin kwamandan kungiyar Saleka da aikata laifukan yaki.
A wani labarin na daban Amurka ta sanya takunkumai a kan shugabannin wasu kungiyoyin ‘yan daba guda biyu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakamakon rawar da suke takawa wajen tunzura jama’a da rikicin kasar mai nasaba da kabilanci da addini.
Sannan takunkumin ya haramtawa Amurkawa da kamfanonin kasar yin hulda da mutanen inda aka kuma rufe asusun ajiyarsu a Amurka.
Rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ya kashe daruruwan mutane tare da raba dubbai da gidajensu.
An zargi mutanen ne da kokarin yamutsa kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki da gudanar a 2015 tare da yin zagon kasa ga jagorancin shugaba Faustin-Archange.