Tsohon dogarin, wanda yanzu shekarunsa 30, yana sanye ne da hular kwano ta ‘yan sanda, duk da cewa an ba shi damar zuwa wurin ne a matsayin mai sa ido.
An zargi fadar shugaban kasa da yin rufa rufa a kan wannan lamari sakamakon gaza kai rahoton aika-aikar Benalla ofishin ‘yan sanda har sai da jaridar Le Monde da ake wallafawa a Faransa ta fito da labarin har da shaidar hoton bidiyo, watanni biyu bayan aukuwar lamarin.
Sanye da bakar rigar kwat, da mayanin fuska, Benalla bai ce da dimbim ‘yan jarida da ke jiran isowarsa kotun na Paris uffan ba.
Ya musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa, yana mai cewa ya ya yi abin da ya yi ne bisa yadda al’amura ke gudana a wurin, da zummar taimaka wa ‘yan sanda kama masu zanga-zangar da ke saba doka.
A wani labarin na daban tashar Alkafil ta bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da zaman karbar gaisuwar Ayatollah Sayyid Hakim Babban malami da Allah ya yi masa rasuwa a Iraki kwanaki tara da suka gabata.
Bayan ga zaman majalisin karbar gaisuwa a Najaf, ana wani majalisin a Karbala tsakanin hubbaren Imam Hussain (AS) da Abul Fadl (AS).
Ayatollah Sayyid Muhammad Said Hakim yana daga cikin manyan malaman mazhabar Ahlul bait (AS) wanda ya rasu a ranar Juma’ar wancan makon da ya gabata, sakamakon tsayawar zuciya.