Iniesta ya lashe kofin duniya daya, da kofunan nahiyar Turai 2 da tawagar kasarsa ta Spain.
Ya kuma lashe kofin sarkin Japan na Emperor Cup, da kuma kofin Super Cup na Japan din da kungiyarsa ta Vissel Kobe, a shekaru 3 da ya shafe a kasar.
Kwanan nan ma tsohon dan wasan barcelona din ya sanya hannu a wani sabon kwantiragin da zai ajiye shi a kungiya har sai ya kai shekaru 40.
A wani labarin na daban kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane ya aike da sakon fatan alkhairi ga Andres Iniesta kan kalaman san a cewa zai bar Barcelona a karshen kakar nan, inda ya ce yana da yakinin cewa dan wasan ne yakamata a ce ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 2010.
Ko da ya ke dai Iniesta mai shekaru 33 bai sanar da Club din da zai koma ba, amma ana ganin yana shirye-shiryen komawa wata kungiyar kwallon kafa da ke China ne.
A shekarar 2010 ne dai yakamata a ce Iniesta ya lashe kyautar Ballon d’Or amma Lionel Messi ya shige gabansa.
Shima dai Pep Guardiola a na shi sakon taya murnar cewa ya yi tarihi ba zai taba mantawa da rawar da Iniesta ya taka a Barcelona ba cikin kusan shekaru 22 da ya yi.
Dama dai a karshen kakar nan ce ake saran Iniesta zai sanar da ritayarsa da ka bugawa kasarsa kwallo bayan taka leda a gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Rasha.