Trump ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya soma gangamin neman sake darewa mulkin ƙasar a zaɓen 2024.
A lokacin wani jawabi a taron shekara-shekara na Republican a New Hampshire, Mista Trump ya zargi gwamnatin Biden da jefa Amurka cikin tasku, yana mai cewa hakan yafi kowa bakanta masa rai da kuma zaburar da shi.
Ya caccaki Mista Biden kan yada yake tunkarar matsalolin baƙin-haure ta iyakar Mexico, yana mai cewa idan ya sake zama shugaba, zai sake dawo da dokokinsa na tsaro a kan iyakoki cikin sa’o’i.
Ya ce zaben 2024 dama ce ta ceto ƙasarmu, kuma muna buƙatar shugaba da zai aiwatar da hakan a ranar sa ta farko.
Mista Trump zuwa yanzu shi kadai ne ya fito ya bayyana aniyarsa ta sake neman kujerar shugaban kasa a badi, koda yake akwai tsoshon gwamnan Florida, Ron DeSantis, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Mike Pense da kuma tsohuwar gwamna a South Carolina, Nikki Haley da ake ganin duk za su shiga wannan takara.
Read More :
Shahadar wani matashin Falasdinawa a Jenin.
Dan siyasar Rasha: Sweden ta cancanci takunkumi na kasa da kasa a cikin lamarin kona Kur’ani.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon: Isra’ila ce ke da alhakin halin da ake ciki a Falasdinu.
Firayim Ministan Yamen: Mun gode wa Iran.