Tottenham ta taso daga baya ta doke Newcastle a tsanake, inda ta koma matsayi na 4 a teburin gasar Firimiyar Ingila.
Tottenham ba ta fara wasan da armashi ba, duba da yadda dan wasan baya na Newcastle Fabian Schar ya saka kwallo a ragarta a minti na 39, kwallon da mai tsaron raga Hugo Lloris ya ji takaicin rashin kama ta.
Tottenham ta mayar da martini ana daf da tafiya hutu ta hannun Ben Davies, wanda ya saka wa kwallon da Son Heung-min ya kawo kai.
Bayan an dawo hutun ne Tottenhm ta shiga gaban Newcastle da kwallon da Matt Doherty ya saka da kai, bayan da Harry Kane ya kawo mai ita, haka kuma suka saka kwallo ta uku ta hannun Son.
Emerson Royal da Steven Bergwijn sun saka kwallo daya kowanne, lamarin da ya sa aka tashi wasa 5-1.
A wani labarin na daban sabon kocin Tottenhm Antonio Conte ya fara jagorantar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara kan Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da kungiyar ta fafata a karkashinsa na gasar Europa a daren ranar Alhamis.
A mintuna 45 na farkon wasan na daren Alhamis da suka fafata sai da magoya bayan Tottenham suka yi tsayuwar ban girma ga Conte ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa dake wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 a ragar Vitesse.
A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere, wanda kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham ad a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera da kwallaye 2-0.