Tor Wennesland; Gina Matsugunan Isra’ila Babban Cikas Ne Ga Shirin Zaman Lafiya.
Jami’in kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Gabas ta Tsakiya ya jaddada cewa, dukkanin matsugunan da Isra’ila ke ginawa a yankunan da ta mamaye ba halastattu ba ne bisa dokokin kasa da kasa, kuma suna kawo cikas ga zaman lafiya.
A rahoton da cibiyar yada labaran Falasdinu ta bayar, Tor Wennesland, kodinetan Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabas ta tsakiya, ya bayyana a taron kwamitin sulhu game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, cewa a watan da ya gabata Isra’ila ta lalata gine-gine 78 na Falasdinawa a yankin C da wasu gine-gine 18 a gabashin Birnin Kudus, wanda hakan yasa mutane kusan 103 da suka hada da yara 50, suka rasa matsugunansu.
Winsland ya bayyana cewa Isra’ila na rusa gidajen Falasdinawa a duk lokacin da take zargin cewa bas u samu izinin gini daga wajenta ba.
READ MORE : Morocco Ta Kirayi Jakadanta A Tunisiya Saboda Karbar Bakuncin Shugaban Polisario A Kasar.
Ya kuma yi kira da a kawo karshen lalata gidajen Falasdinawa da matsugunansu, tare da amincewa da tsare-tsaren da Falasdinawa za su gina nasu gidajen ba tare da wata takura ko wani tarnaki ba.