Wata kungiyar ta’addanci da ke Mali, mai alaka da Al-Qaeda ta dau alhakin harin da aka kai kasar Togo a watan da ya gabata.
Kungiyar Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin tana ta fadada ayyukanta a cikin ‘yan kwanakin nan, inda take barazana ga arewacin kasashen Benin, Ivory Coast, Ghana da Togo.
Gwamnatin Togo ta tabbatar da harin ta’adancin da ya auku ranar 11 ga watan Mayu a garin Kpekankandi, kusa da iyaka da Burkina Faso, inda ‘yan ta’adda ke da yawa.
Hukumomin Togo sun ce dakarun Togo 8 ne suka mutu, 13 suka samu raunuka.
Wata majiya daga gwamnatin Togo ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa kimanin mahara 60 bisa babura ne suka kai wa dakarun Togo hari.
A wannan labarin na daban gwamnatin ta tabbatar da kisan mahara 15 a wani farmakin ta’addanci da suka kai kan dakarun kasar da ke aikin sintiri a iyakar Burkina Faso cikin makon jiya wanda ya kashe sojoji 8 tare da jikkata wasu 13.
Ministan tsaron kasar Janar Damenhame Yark ya ce yayin farmakin ‘yan ta’addan na ranar 10 zuwa 11 ga watan nan, Sojinsu sun yi nasarar kashe 15 daga ciki koda ya ke sun yi asarar dakarunsu 8 baya ga wasu 13 da suka jikkata.
Rahotanni sun ce mahara fiye da 60 haye a babura ne suka farwa Sojojin da ke aiki a garin Kpinkankandi akan iyakar Togo da Burkina Faso tare da hallaka 8 daga ciki.
Cikin jawabinsa ta gidan talabijin, Janar Yark ya ce tuni aka isar da gawarwakin Sojojin yankunansu don birnesu.
Dubunnan Sojin Togo ne yanzu haka aka girke a yankin arewaci don katange barazanar tsaron da kasar ke fuskanta daga maya masu ikirarin jihadi da ke kokarin tsallaka mata daga kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.
Ko a watan Nuwamban bara sai da Sojin Togo suka dakile wani farmakin ta’addanci da mayaka masu ikirarin jihadi suka nufaci kai wa kauyen Sanloaga.
Harin na makon jiya dai shi ne karon farko da ake asarar rayuka sanadiyyar ta’addanci a kasar ta Togo duk da yadda makamantan hare-haren ke ci gaba da tsananta tsakanin kasashen yammacin Afrika.
Alkaluma na nuna yadda kasashen yammacin Afrika suka fuskanci hare-hare fiye da dubu 5 da 300 cikin shekaru ukun baya-bayan nan wadanda suka haddasa asarar rayuka dubu 16.