Kwanaki 5 bayan da wani matashi dan bindiga mai shekaru 18 ya bude wuta kan mai uwa da wabi a wata makarantar Firamare ta Robb a Uvalde dake jihar Texas na Amurka, tareda kashe dalibai yara 19 da malamai biyu,shugaban Amurka Joe Biden zai ziyarci yankin a yau lahadi.
Harin makarantar firamare ta Robb da ke garin Uvalde na Latino, shi ne hari mafi muni da ake kai wa makarantun Amurka tun bayan da wani dan bindiga ya kashe yara 20 da manya shida a makarantar Sandy Hook da ke Newtown, Connecticut, a watan Disambar shekarar 2012.
Kuma ya zo ne kwanaki 10 kacal bayan da wani kazamin harin wariyar launin fata da aka kai a wani babban kanti na Buffalo da ke birnin New York, wanda ya kara yawan kashe-kashen jama’a na tsawon shekaru a coci-coci da makarantu da shaguna a kasar ta Amurka.
Ziyarar ta Shugaban na Amurka a Uvalde ta texas na zuwa a wani lokaci da ake ci gaba da caccar baka dangane da mallakar bindigogi a Amurka.
A wani labarin daga Burkina Faso, dubban magoya bayan tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ne suka fito don nuna damuwar su ganin ci gaba da tsare tsohon shugaba da majalisar sojin kasar ke yi yanzu haka.
Magoya bayan tsohon Shugaban sun gudanar da zanga-zangar lumanar ce a birnin Ouagadougou.
Yayin jawabi ga manema labarai sun gargadi majalisar sojin kasar da ta gaggauta kawo karshen tsare tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore da aka kifar ranar 24 ga watan janairun shekarar nan, mudin hakan ba ta samu ba to za su fadada wanan zanga-zanga zuwa sauren yankunan kasar ta Burkina Faso 45.
Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta Ecowas ta shiga tattaunawa da majalisar sojin kasar ta Burkina Faso,na ganin lamura sun daidata,tun bayan juyin mulkin watan janairu,ba tareda cimma wani muhimin sauyi ba yanzu haka