Wani matashin dan bindiga mai shekaru 18 ya bude wuta kan mai uwa da wabi a wata makarantar Firamare da ke Texas na Amurka, inda ya kashe dalibai yara 19 da malamai biyu.
Matashin da ya kai hari makarantar Robb Elementary School mai suna Salvador Ramos ya shiga dakunan karatu daya bayan daya yana harbi, kafin jami’an tsaro su yi nasarar bindige shi har lahira.
Hari mafi muni kan makarantu
Harin makarantar firamare ta Robb da ke garin Uvalde na Latino, shi ne hari mafi muni da ake kai wa makarantun Amurka tun bayan da wani dan bindiga ya kashe yara 20 da manya shida a makarantar Sandy Hook da ke Newtown, Connecticut, a watan Disambar shekarar 2012.
Kuma ya zo ne kwanaki 10 kacal bayan da wani kazamin harin wariyar launin fata da aka kai a wani babban kanti na Buffalo da ke birnin New York, wanda ya kara yawan kashe-kashen jama’a na tsawon shekaru a coci-coci da makarantu da shaguna.
Dokar Mallakar bindiga
Shugaban Amurka Joe Biden wanda yayi Allha wadai da harin na garin texas, ya sake jadda bukatar garambawul ga dokokin mallakar bindiga, a wani jawabi ga al’ummar kasar sa’o’i bayan harin.
A wani labarin na daban wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a taron kade-kade da raye-raye a birnin Miami na jihar Florida da ke Amurka, inda akalla aka tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da kimanin 20 ke cikin mawuyacin hali.
Harin ya auku ne a harabar wani katafaren dakin gudanar da bukukuwa a wani dandali da ke birnin Miami, inda akasari mutanen kasar Cuba masu rufan asiri ke rayuwa.
Rahotanni sun ce, maharan sun sanya manyan riguna tare da rufe fuskokinsu kafin tarwatsa taron jama’ar da harsashai.
Majiyar ‘yan sanda ta ce, ‘yan bindigar sun iso ne a cikin wata motar SUV kirar Nissan Pathfinder, inda mutane uku daga cikinta suka fito, sannan suka fara bude wuta kan taron jama’ar.
Tuni ‘yan bindigar suka tsere bayan aika-aikar, kuma kawo yanzu babu cikakken bayani game da makasudin kadddamnar da farmakin kan mahalarta bikin.
A halin yanzu, mutane 20 da suka samu raunin harsasahai a harin na kwance a asibiti rai-kwa-kwai mutu-kwakwai a cewar ‘yan sanda.
Jami’an tsaro na neman hadin kan al’ummar yankin wajen farautar wadannan mahara.
Amurka na fama da matsalar hare-haren bindiga, lamarin da ke haddasa asarar dubun dubatan rayuka a duk shekara a kasar.