Tel Aviv ta tuntubi Majalisar Dinkin Duniya da Masar domin dakile harin da Falasdinawa ke kaiwa
Domin hana duk wani harin da kungiyoyin gwagwarmaya zasu iya kaiwa, Tel Aviv ta kulla alaka ta wayar tarho da masu shiga tsakani.
Gwamnatin Sahayoniya ta kulla alaka ta wayar tarho da Masar da UNIFIL (Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kudancin Labanon) domin dakile duk wani tashin hankali a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.
Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu a yau ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da martani kan laifukan sahyoniyawan.
Mayakan gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kai hari a yankuna daban-daban na zirin Gaza a wani harin ba zata da ake kira “Garkuwa da Kibiya”.
Ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta sanar da cewa, Falasdinawa 13 ne suka mutu a wannan harin, sannan sama da mutane 20 da suka hada da mata da yara da dama suka jikkata.
A cikin wannan hari gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi shahada uku daga cikin kwamandojin kungiyar Jihad Islamiyya da matansu da wasu ‘ya’yansu.
An aiwatar da wannan aika-aika na gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza tare da hadin gwiwar sojoji da kuma jami’an tsaron cikin gida na wannan gwamnati (Shabak) tare da yin amfani da mayaka 40.