Sama da mutane 70 ne suka bace a tekun Mediterrenean bayan da wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure da ya taso daga Libya ya nutse a makwabciyar kasar Tunisia.
Kasar Libya ta zama wata babbar tashar da bakin haure da ke neman isa Turai, wanda ta zama hanya.
A wani labarin na daban shugaban Kungiyar agaji ta Red Cross a Duniya Francesco Rocca ya cacaki kasashen Turai saboda abinda ya kira yadda suke nuna banbanci wajen kula da bakin da suka fito daga Ukraine da kuma wadanda suka fito daga nahiyar Afirka.
Rocca ya ce tabbas akwai nuna harshen damo tsakanin wadannan kasashe wajen yadda suke karbar bakin da suka fito daga wadannan bangarori biyu, ganin yadda suke rungumar wadanda suka fito daga Ukraine da kuma nuan kyama ga wadeanda suka fito daga Afirka.
Shugaban yace banbanci tsakanin mutumin da ya tsere daga Donbas dake kasar Ukraine da kuma wanda ya gudu daga yankin da ake fama da tashin hankalin book haram.
Yayin da yake yabawa al’ummomin kasashen Turai akan yadda suke rungumar Yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine, Rocca yace abin takaici baki kadan ne da suka fito daga Afirka ke samun irin wannan tarba bayan tsallake tekun Miditereniya mai dauke da hadari.
Kasashen duniya sama da 150 suka rattaba hannu akan yarjejeniyar magance matsalar karbar bakin dake tserewa daga kasashen da ake fama da tashin hankali a duniya.