Maaikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran dake babban birnin Tehran ta tabbatar da cewa gwamnatin Iran ba zata taba biyewa bukacin amurka na son kai ba a tattaunawar dake gudana a birnin vienna.
A ta bakin mai magana da yawun ma’ikatar harkokin wajen Iran din Saeed Khadib Zadeh ya bayyana cewa hatta tsaikon da aka samu atattaunawar ya samu asali ne daga son kan da amurka take nunawa a yayin tattaunawar.
Shima ministan harkokin wajen Iran din Amir Abdullahiyan a wata tattaunawa kan yadda za’a farfadon da yarjejeniyar nukiliayar 2015 din ya bayyana cewa zari gami da son kan da amurka ta nuna a wajen tattaunawar shine ya kawo tsaiko a kokarin da akeyi na cimma matsayar wacce zata amfani kowa amma minsitan ya tabbatar da cewa Tehran ba zata taba amincewa da wannan bukatu na amurkan ba.
”Idan a kwai tsaiko a tattaunawar vienna ya samo asali ne daga bukacin son kai da amurka ta gabatar a wajen tattaunawar” kamar yadda Amir Abdullahiyan ya wallafa a shafin sa na tuwita.
اگر مکثی در روند مذاکرات وین دیده می شود، بدلیل زیاده خواهی طرف آمریکایی است. وزارت امور خارجه در جهت کسب عالی منافع ملت و رعایت خطوط قرمزها با قدرت و منطق عمل می کند. هرگز زیر بار زیاده خواهی آمریکا نخواهیم رفت. اگر کاخ سفید واقع بینانه رفتار کند، توافق دست یافتنی است.
— H.Amirabdollahian امیرعبداللهیان (@Amirabdolahian) April 4, 2022
Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar harkokin wajen Iran tana amfani da karfin ikon da take dashi da kuma hikimomi domin tabbatar da abinda ya kamata a tattaunawar tare da kiyayen jan layin ta inda ba zata bari a tsallaka mata ba.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana cewa, Iran da gungun kasashen P4+1 sun cimma matsaya mai kyau a tattaunawar madamar amurka zatayi abinda ya kamace ta.
An dingi tattaunawa a babban birnin kasar australiya tsakanin kasashen da abin ya sahafa duk domin farfado da yarjejeniyar wacce aka fi sani da ”JCPOA” wacce amurka karkashein jagorancin tsohon shugaban ta donald trump ta fice daga yarjejeniyar.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran a wani taron manema labarai daya gabatara a birnin Tehran ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran tana kan matsayi mai kyau kuma ba zata amince da duk wata matsaya da ta sabawa maslahar Iraniyawa ko ta taka jan layin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran ba.