Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce ta fara gudanar da bincike kan rahotannin kashe fararen hula da dama da ake zargin sojojin kasar da kuma sojojin hayar wani kamfanin tsaron Rasha da aikatawa.
Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil’adama, Michelle Bachelet, ta yi Allah wadai da take hakkin bil’adama da aka yi a kasar, da suka hada da kashe ‘yan ba ruwan mu da cin zarafin mata, da tawagar kungiyoyin ‘yan tawaye da kuma sojojin kasar da kawayensu na Rasha ke aikatawa.
A wani labarin na daban kuma A karon farko tsohon jagoran ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ake zargi da aikata laifukan yaki da kuma ta ke hakkin bil-Adama Maxime Makom, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Makom mai shekaru 43, a ranar Litinin ne Chadi ta mika shi ga hukumomin kotun ta ICC da ke birnin Hague a Holland, inda ya tabbatar da cewar an shaida masa lafukan da ake zargin sa da aikatawa.
Lauyan sa ya bayyana cewar, hukumomin Chadi sun azabtar da Makom a tsawon lokacin da ya shafe a hannunsu ta yadda suka rika ciyar da shi lalataccen burodi baya ga barinsa ya kwana a kasa ba gado.
An dai tsaida ranar 31 ga watan Janairun badi domin fara sauraron karar.
Rikicin da ‘yan tawayen Seleka da kuma Balaka suka haifar a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma sanya wasu rasa muhallan su.
Tuni dai aka gurfanar da biyu daga cikin wadanda suka jagoranci tawaye a kasar, Patrice Edouard Ngaissona da kuma Alfred Yekatom a gaban kotun, yayinda aka tsaida watan Satumba don fara shari’ar Mahamat Said Abdel Kani wanda ake zargi a matsayin kwamandan kungiyar Saleka da aikata laifukan yaki.