Babban sakatare a ofishin tsare-tsare da bunkasa juba jari na kasar Tanzania Tausi Kida, ya ce kasar Sin ce kan gaba a fannin zuba jarin waje na kai tsaye ko FDI a kasar, wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa ci gaban Tanzania.
Mista Kida, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a birnin Dar es Salaam, yayin kammala taron tattaunawa na yini guda na zuba jari tsakanin Sin da Tanzania, da taron habaka harkokin cinikayya da zuba jari na Sin (Jinhua) da Tanzania.
A cewar jami’in, daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Disamban 2023, cibiyar zuba jari ta Tanzania, ta yi rajistar ayyukan zuba jari daga Sin wadanda yawansu ya kai 256, kana kimarsu ta kai kimanin dala biliyan 2.5.
Kaza lika, sassan da ayyukan suka shafa sun hada da na samar da hajoji, da gine-ginen kasuwanci, da noma, da sufuri da kuma fannonin bayar da hidima. (Saminu Alhassan)
Tinubu Ya Karrama Sojojin Najeriya Da A Ka Kashe
A wani labarin na daban shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bai wa sojoji 17 da aka yi wa kisan gilla a yankin Neja Delta lambar girmamawa ta kasa da kuma alkawarin gina wa kowanne gida a inda suke so tare da bai wa ‘yayansu tallafin karatu har zuwa matakin jami’a.
Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin gudanar da jana’izar sojojin sojoji 17, inda ya bayar da umarnin cewar hukumomin soji su tabbatar da cewar an biya hakkokin wadannan soji nan da wata uku.
Tinubu ya bayyana cewar shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya masa bayani a kan irin gagarumar gudumawar da Laftanar Kanar Ali, kwamandan sojin da aka kashe ya bayar wajen yaki da Boko Haram da kuma ‘yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma, kafin mayar da shi yankin Neja Delta.
Shugaban ya ce a madadin Nijeriya yana mika sakon jinjina ga Kanar Ali saboda yadda ya bayar da gagarumar gudumawa a rundunar sojin har zuwa lokacin da aka masa kisan gillar.
Tinubu ya ce a matsayinsa na babban kwamandan sojin Nijeriya baki daya, yana sane da irin gudumawar da bajintar da sojojin suka bayar wajen tabbatar da tsaron Nijeriya.
Shugaban ya ce duniya na sane da rawar da sojojin Nijeriya ke takawa a Afirka da kuma wasu sassan duniya, saboda haka ba za su bar iyalansu su taggayara ba.
DUBA NAN:Kasheem Shettima: Naira Zata Cigaba Da Farfadowa
Jana’izar ta samu halartar manyan hafsoshin tsaro da ministoci da iyalan sojojin da aka kashe.