Ministan harkokin kasashen wajen Iran, Amir Abdullahian ya bayyana cewa, Iran tana maraba da tattaunawar diflomasiyya domin farfado da yarjejeniyar (JCPOA) amma Jamhuriyar Musulunci Ta Iran tana fatan Amurka zata maida kai kuma tayi da gaske domin samar da natija mai dorewa a tattaunawar da akeyi tsakanin kasashen da abin a shafa.
A tattaunawar sa ta wayar tarho da mai kula da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar turai, Josep Borrell, minsitan harkokin wajen Iran din ya bayyana cewa Iran tana maraba da bibiyar hanyoyin diflomasiyya domin cimma matsaya amma dole amurka ta maida hankali domin gudun samun cikas.
A ranar talatar data gabata mai da Josep Borrell ya bayyana cewa yana aiki a kan wasu sabin hanyoyi na musamman domin cimma matsaya.
Minisatan harkokin wajen Iran ya tabbatarwa da abokin aikin sa na kungiyar tarayyar turai cewa, amurka a kullum tana bayyanar da cewa tana goyon bayan bibiyar hanyoyin tattaunawa domin smar da matsaya amma idan da gaske take ya kamata a tabbatar da hakan a aikace ne.
Babu tantama dangane da niyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samar da ciakkiyar matsaya mai inganci kuma wacce zata tabo dukan bangarori, inji Amir Abdullahian kuma ya godewa abokin aikin sa na kungiyar tarayyar turai gami da mataimakin sa Enrique Mora bisa kokarin su na tabbatar da cewa an samu masalaha tsakanin Iran da kuma sauran kasashen turai.
A bangaren Borell ya bayyana cewa, lallai Iran ta bayyanar da cikakken niyyar tadomin samar da matsaya a wannan tattaunawa kuma ya bukaci hakan ya zama dalilin da za’a samu matsaya mai dorewa a wannan karon.
Ita dai Amurka a mayun shekarar 2015 ta sake kakaba takunkuman tattalin arziki da sauran bangarori a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta sanya kafa ta fice daga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da sauran kasashe masu fada aji na duniya