Kamar yadda kafar sadarwa da Mehr News ta rawaito domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Sayyida Fadima (A.s), sa’annan kuma da tunawa da zagayowar ranar shahaadar Janaral Janaral Kasim Sulaimani samari daga kasashe mabambanta zasu gudanar da tattakin daga titin fiyambare a’azam zuwa samallachi mzai tsarki na Jamkaran.
Kamar yadda ta rawaito jaridar Mehr News ta tabbatar da cewa wannan tattakin za’a soma shine da misalin karfe ukku na yammacin ranar talata 2 ga watan janairu, wanda ake sa ran matasa masu neman ‘yanci zasu tattaka domin tunawa duniya shahadar Sayyida Fadima (A.S) diyar manzon Allah (s.a.w.w) da kuma shahadar Janaral Kasim Sulaimani wanda aka kashe a kusa da filin tashin da saukar jirage na birnin Bagadazan Iraki a waatan janairun shekarar 2020.
Sanarawar da Mehr News ta sanar cewa, tawaga tawaga ta motoci, babura suma za su iya bi ta hanyar Ali Yasin domin shiga cikin wannan tattaki, sa’annan za su iya bi ta hanyoyi mabambanta na birnin Qom mai tsarki domin isar da kan su ga wannna tattaki d za’a gudanar.
A da dama dai ana ta nuna alhini gami da shirya tarurruka domin tunawa da ranar zagayowar shahadar Sayyida Zahra (S.a) gami da Shahadar Janaral Kasim Sulaimani musamman da yake wannan shekarar ta zo a lokacn da Isaraila ke luguden wuta a kan raunana Falasdinawa.
KASIM SULAIMANI dai na zaman Janaral din soja da Iraniyawa suka fi nunawa Soyayya sakamakon alakanta shi da ceto kasar su gami da samo musu izza a idanun duniya.