Tattara sojojin jiran ko- ta-kwana masu yawan gaske da kwaso dimbin mutane daga kasashe da wurare da rudanin da yakin ya jawo ya matukar girgiza tattalin arzikin kasar Isra’ila, inda ya jawo tasiri na koma-bayan harkokin kasuwanci a kasar.
Darajar kudin kasar, wato shekel ya yi karyewar da bai taba yi ba a shekara 14, sannan ma’aunin kasuwar hannun jarin kasar ya koma kashi 10 a bana. Hoto AA
A makon jiya ne Firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu ya yi hasashen samun yanayin zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya saboda yadda a cewarsa Isra’ila take kara samun karbuwa a yankin.
Amma zuwa yanzu kuwa, duba da yadda yakin Isra’ila da Gaza ya shiga mako na hudu, wannan kudurin da alama ya sha ruwa.
Tattara sojojin jiran ko- ta-kwana guda 360,000 da kwaso ’yan Isra’ila guda 250,000 kamar yadda kididdigar da sojojin Isra’ila suka bayar ta nuna, ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da dama a kasar.
An rufe wuraren cin abinci da otel-otel da dama. Kamfanonin jiragen sama sun tsagaita jigilar fasinja zuwa Isra’ila, masu yawon bude ido da dama sun fasa zuwa kasar.
An kulle wata babbar tashar iskar gas a kasar, gonaki da dama sun lalace saboda rashin ma’aikata, sannan dubban ma’aikata sun rasa ayyukansu.
Isra’ila ta rantse sai ta ga bayan kungiyar Hamas a Gaza, wadda ta kashe mata mutum 1,400, sannan ta yi garkuwa da sama da 240 a harin da ta kai Kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba.
Hare-haren jiragen sama Isra’ila sun tarwatsa tare da kashe sama da mutum 8,000 a Gaza kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta sanar a Gaza.
Tattalin arzikin Isra’ila na dawowa da ƙarfi bayan yake-yaken da ta yi a baya, amma da alama wannan karon za a dauki lokaci ba a watstsake ba, watakila a dauki watanni, domin burin sojojin kasar shi ne kawo karshen Hamas, ba wai dakile mayakan ba.
Fadadar yakin shi kansa wata barazanar ce daban. Yanzu haka Isra’ila tana wasu yake-yaken guda uku ta karkashin kasa-Da Lebanon, da yankin West Bank da ta mamaye da kuma Syria.
Dadewa tana fuskantar yake-yake daban-daban a lokaci daya zai sa tattalin arzikin ya dade bai farfado ba kamar yadda suka saba gani a baya.
Sannan ko kafin a fara yakin, tattalin arzikin kasar ya riga ya fara taɓarɓarewa tun bayan yunƙurin Netanyahu na rage karfin bangaren shari’a, wanda bai samu karbuwa ba sosai.
Tallafi kadai ba zai iya gyara tattalin arzikin ba
Ma’aikatar Kudi ta Isra’ila ta bayyana tsarin tallafin inganta tattalin arziki da a ciki akwai bayar da tallafin Dala biliyan 1 ga ’yan kasuwar da yakin ya shafa.
Masu sharhi sun ce wannan ba zai yi wani kataɓus ba, sannan suka buƙaci a karkata wasu biliyoyin dalolin zuwa ga wasu hanyoyin daban na shirya sabuwar yarjejeniya zaman lafiya tsakanin masu ra’ayin Yahuduwa zalla da masu maraba da baki.
A makon nan ma, wani taron masana tattalin arziki su 3,000 sun yi kira ga Netanyahu da Ministan Kudin Isra’ila Bezalel Smotrich da “Su bi a hankali!”
“Rudanin da Isra’ila ta shiga yana bukatar tunani mai kyau ne wajen yin abubuwan da kasar ta fi bukata da kuma karkatar da kudade zuwa magance matsalolin da yakin ya haifar da taimakon wadanda yakin ya shafa da kuma gyara tattalin arziki,” in ji su a wata wasika, inda a ciki suka yi hasashen kudaden da ake kashewa a yakin zai iya cin sama da biliyoyin daloli.
Source: TRT HAUSA