A ranar 15 ga watan nan, taron kolin MDD kan batun kasuwanci da ci gaba wato UNCTAD, ya fidda rahoton kasuwanci da ci gaba na shekarar 2021.
Rahoton ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya ba da matukar mamaki kuma ya jure dukkan wahalhalun karayar tattalin arziki a shekarar bara.
A lokacin barkewar annoba, kasar Sin ta aiwatar da tsarin kafa dokar kulle da gudanar da gagarumin aikin gwaje-gwajen cutar, tare kuma da daukar dukkan matakan kariya mafiya dacewa, kana ta gaggauta samar da riga-kafi domin dakile bazuwar annobar.
A bangaren bukatu kuwa, kasar Sin ta kiyaye tsarin ayyukan zuba jari na cikin gida. Bayan dokar kullen, bukatun kayayyakin da masana’antu ke samarwa ta yi matukar karuwa, wanda hakan shi ma ya taimakawa kasar Sin wajen farfadowa. Idan an kwatanta da mafi yawan kasashen duniya, kasar Sin ta riga ta farfado tun da wurwuri, kana tana ta samun saurin bunkasuwa a fannin fici da shigin hajoji.
A watanni shidan farko na bana, alkaluman yanayin gudanarwar kasuwancin kasar Sin na kowane wata ya karu da sama da kashi 10% inda ya zarta matakin gabanin barkewar annobar.
Tattalin arzikin shiyyar gabashin Asiya shi ne mafi karfi a shekarar 2020. An yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar gabashin Asiya zai iya kaiwa kashi 6.7% a shekarar 2021, wanda galibi kasar Sin ke jagorantarsa. Taron kolin kasuwancin da ci gaba na MDD ya yi hasashen cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai iya kaiwa kashi 6% a wannan shekara.
Domin cin moriya daga farfadowar bukatun kasa da kasa da irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen samar da kayayyaki a duniya, kamar kayayyakin latironi a fannin fasahar sadarwa, da kayayyakin kiwon lafiya da riga-kafi, kasar Sin ta bayar da kwarin gwiwa mai karfi ga kamfanonin fitar da kayayyaki zuwa ketare.
Bugu da kari, UNCTAD ta yi hasashen cewa, bukatun cikin gidan kasar Sin zai farfado sannu a hankali, kana taimakon da gwamnatin Sin ke ci gaba da baiwa sabbin ayyuka a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa shi ma zai taimaka wajen tabbatar da fadada ingantaccen tsarin kashe kudaden gwamnati.