Tashar
Alghadir ta bayar da rahoton cewa, a yau ne aka gudaar da Taron janazar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Sayyid Muhammad Sa’id Hakim a birnin Najaf na Iraki, bayan da Allah ya yi masa rasuwa a ranar Juma’a da ta gabata.
An bizne gawar marigayin a wata makabarta da ake bizne iyalan Hakim, wadanda suka hada da manyan malamai da aka yi a kasar Iraki, makabartar da take kusa da hubbaren Imam Ali (AS) a birnin Najaf.
Taron janazar ya samu halartar manyan malaman addini daga sassa na kasar Iraki, da kuma shugabannin kabilun larabawan kasar da kuma sauran kabilu, gami da jami’an gwamnatin kasar.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran
Al’ain ya bayar da rahoton cewa, kwamitin kula da masallacin manzon Allah (SAW) ya sanar da cewa, an dawo da taron karatun halqa da aka saba gudanarwa a masallacin mai alfarma.A ranar laraba da ta gabata ce aka gudanar da lacca ta addini ta farko a masallacin manzo (SAW) tun bayan bullar cutar corona, inda aka dakatar da laccoci da sauran bayanai da aka saba yi an addini a cikin wannan masallaci, saboda dalilai na kiwon lafiya.
Sheikh Abdulrahman Al-sudais ne ya gabatar da laccar, wanda ya yi bayani kan muhimman abubuwan da suka rataya a kan musulmi su kiyaye musamman lokacin da aka samu bullar annoba irin wadda ta game duniya.
Tun daga lokacin da cutar ta bulla ne dai aka dakatar da karatun halqa da ake a cikin masallacin ma’aiki (SAW) wanda mutane suke yin karatun littafai a wajen malamai na fikihu da hadisi da kuma tafsiri da sauran bangarori na ilimi.