Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Alahad cewa, a yau an gudanar da taron janazar babban malamin addini Allamah Abdulamir Qabalan a birnin Beirut na kasar Lebanon.
A ranar Litinin da ta gabata ce Allah ya yi wa Allamah Qabalan rasuwa bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Tun bayan bacewar shugaban majalisar mabiya mazhabar ahlul bait a kasar Lebanon Imam Musa Sadr, a kasar Libya, bayan da tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi ya gayyace shi, mataimakinsa Allamah Qabalan ya ci gaba da jagorantar lamurran majalisar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron janazar a yau Talata akwai wakilan shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon, baya ga haka kuma wasu daga cikin ministoci gami da malaman addini na shi’a da sunnah sun halarci wurin.
Allamah Abdulamir Qabalan dai ya kasance mai goyon bayan hadin kan al’ummar kasar Lebanon, wanda hakan ne ya bashi matsayi na musamman da girmamawa daga dukkanin al’ummar kasar.
Baya ga haka kuma ya kasancea sahun gaba wajen mara baya ga gwagwarmayar al’ummar kasar wajen yaki da mamayar da Isra’ila ta yiwa kasar har zuwa lokacin da kungiyar Hizbullah ta fattaki Isra’ila daga Lebanon.
Haramtacciyar kasar isra’ila dai ta jima da kokarin kutse cikin kasar labanon amma sakamakon kokari gami da goyon bayan gwagwarmayar kasar da manyan malamai irin su Allamah Abdulamir Qabalan, isra’ilan bata iya cimma burin ta na raba kana al’ummar kasar ta labanon ba.
Rashin irin su Allamah Qabalan ba karamin rashi bane ga al’ummar labanon dama duniya baki daya, hakan tasa al’umma daga sassan duniya daban daban suke bayyana sakon ta’aziyyar da kuma fatan Allah ya karbi uzurin wannan babban malami.