Taron Astana Ya Kara Karfafa Alaka Tsakanin Tehran, Ankara Da Moscow.
An kammala taron Astana kan batun kasar Siriya, karo na bakwai da Iran ta karbi bakunci a jiya Talata.
Taron wanda na wannan karon ya kara karfafa alaka tsakanin kasashen Iran, Rasha da kuma Turkiyya.
Yayin wata ganawa tsakanin shugaba Putin na Rasha da jagoran juyin juya halin musulimci na Iran, kasashen biyu sun jadadda anniyarsu ta karfafa ta fuskar tattalin arziki da kuma soji.
Kasashen biyu dake goyan bayan shugaba Bashar Al Assab na Siriya, sun kuma bukaci ficewar Amurka a yankin arewa maso gabashin Siriya da dakarun kurdawa ke rike da, wanda kuma hakan zai faranta wa Turkiyya matuka duba da shirin da take na kaddamar da farmakin soji kan kurdawan da take alakantawa da ‘yan ta’adda.
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa kai hari a arewacin Siriya zai iya cutar da Turkiyya da Siriya dama yankin baki daya, sannan hakan zai baiwa ‘yan ta’adda damar cin karensu babu babbaka.
Jagoran ya bayyana hakan ne lokacin da yayi wata ganawar da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan jiya Talata.
Yayin ganawar Jagoran ya jadadda mahimancin karfafa alaka ta fuskar kasuwanci tsakanin kasashen Turkiyya da Iran.
Jagoran ya kuma alakanta ‘yan sahayoniya, a matsayin ummul aba’isin duk wani rikici dake tsakanin kasashen musulmi.