Sojojin Isra’ila sun ware wasu yankuna inda suka raɗa musu sunan “yankunan kisa” a Gaza, suna ɗana tarkon kisa ga duk wanda ya taka ƙafarsa a yankunan, in ji wani bincike da Haaretz ta gudanar a kwanan baya.
“Gazawar sojojin na yin aiki da dokokin aikinsu ya janyo sojoji na kashe fararen hula ba gaira ba dalili, kuma ba a hukunta su”
Sojojin Isra’ila sun samar da “yankunan mutuwa” a ciki da wajen Gaza da manufar kashe Falasɗinawa da suka taka ƙafarsu a wuraren, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito majiyoyin sojin na faɗa.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha yabon sojojin ƙasar da cewa “Sojoji mafi aiki da ƙa’idoji a duniya”.
Sai dai kuma, dalilai da hujjojin da aka samu sun saɓa da kalaman nasa. Abubuwan da sojojin Isra’ila ke yi sun sa Amurkawa na sanya alamar tambaya kan biliyoyin dalolinsu na haraji da ake kashe wa sojojin Isra’ila suna cin zarafin Falasɗinawa.
A baya-bayan nan Amurka ta amince a aike da bama-bamai masu nauyin fam 2000 da ƙarin wasu makamai zuwa Isra’ila.
Duk da bayar da tabbaci daga gwamnatin Biden kan cewa za a yi amfani da makaman bisa dokokin ƙasashen duniya, rahoton binciken na jaridar Isra’ila ta Haaretz ya yi ƙarin haske kan asalin ayyukan da sojojin da Amurka ke ɗaukar nauyi suke yi a Gaza.
Wani jami’in ma’ajiyar kayayyakin soji da jaridar Haaratz rta ruwaito ya bayyana cewa “yankin yaƙi” na da muhimmanci a Gaza. Na nufin wani yanki da aka jibge sojoji, a gidajen da babu kowa, sannan aka bar shi babu alamun akwai sojoji a ciki. Wani sunan da ake sanya wa waɗannan wurare shi ne ‘yankunan kisa’
Jami’in ya ƙara da cewa a kowanne yanki na kisa ko yaƙi, kwamandoji ne ke bayyana yadda za a yi aiki, yawancinsu na kawo dokokinsu na kansu.
DUBA NAN: Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Musanta Cin Bashi
Jami’in ya ce “Da zarar mutane sun shiga yankunan ana bayar da umarni a harbe su, ko da kuwa ba sa ɗauke da makami.”