Cibiyar ta sanar da cewa, an tarjama hudubobin da suke yin magana a kan kare hakkokin bil adama da kuma hakkokin mata a mahanga ta addini.
Wannan tarjama an mayar da ita ta zama littafi mai zaman kansa, wanda a halin yanzu an buga kwafi 1000 na littafin, kuma za a ci gaba da buga shi domin amfanin mutane.
A wani labarin na daban mai kama da wannan tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Muhamamd Al-na’is dattijo ne dan shekaru 70 da haihuwa, wanda ya hardace kur’ani shekaru biyar da suka gabata a cikin tsufansa.
Ya ce tun a shekarun baya ne ‘yan ta’adda da suka addabe su a kauyensu, hakan yasa ala tilas suka yi gudun hijira suka kaurace ma kauyen.
Muhammad ya ce,a lokacin gudun hijirar ne ya samu matsalar gani sakamakon irin makaman da ‘yan ta’adda suka rika harbawa a kan jama’a musamamn wadanda basu goyon bayansu.
Sakamakon haka ne kuma ya rika amfani da rikoda mai amfani da kaset wajen sauraren karatun kur’ani, kuma a cikin wadanann shekaru kasa da biyar ne ya hardace kur’ani mai tsarki baki daya.
Wannan dattijo dai ana bayyana shi da cewa yana da kaifin basira wajen rike komai a kwakwalwarsa, inda ya hardace suanayen dukaknin shugabannin kasashen duniya, da kuma sunayen manyan tekuna na duniya.