Kungiyar Turai za ta kira taron gaggauwa don sake tattaunawa dangane da zaman tankiyar da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ne jagoran wata kasar Turai na baya bayan nan da yake yunkuri na diflomasiya don samo masalaha a game da wannan rikici, a yayin da a yau zai yi wata tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin.
Wasu jami’an kungiyaar Tarayyar Turai sun ce kungiyar na dakon sakamakon tattaunawar da Scholz zai yi da Putin, suna mai cewa akwai yiwuwar kiran wani taron gaggawa idan bukatar hakan ta taso a zaman da jagororin Turai za su yi da na Africa a Brussels.
Tarayyar Turai tare da kawayenta sun sha alwashin kakaba wa Rasha takunkumai idan har ta aiwatar da niyarta ta mamayar Ukraine.
Rasha, wadda ta musanta cewa tana shirin mamayar Ukraine, ta nuna alamun za a samu masalaha bayan da a ranar litinin ta nuna cewa kofarta a bude take don tattaunawa.
Zaben nata ya zo ne mako guda bayan mutuwar shugaban majalisar dokokin EU David Sassoli, wanda dama ke dab da sauka daga mukaminsa bisa yarjejeniyar raba madafun iko.
Sabuwar shugabar ta dauki kanta a matsayin mai goyon bayan daidaiton jinsi da kuma rajin da take yi na kare hakkin mata amma kuma zafafa matsayarta na yakar zubar da ciki ya janyo suka daga abokan hamayya.
Zubar da ciki haramun ne a Malta, kasar da yawancin al’ummarta ke bin darikar Katolika kuma ko a watan Yunin da ya wuce, Metsola ta kada kuri’ar rashin amincewa da wani rahoto da ya bukaci dukkan kasashe mambobin EU su halasta zub da ciki.
Da take ajawabi a zauren majalisar, Roberata Metsola, ta ce za a bawa shirin yaki da matsalar sauyin yanayi a Majalisar Tarayyar Turai fifiko.