Kungiyar tarayyar Turai ta tallafa wa Jamhuriyar Nijar da kudaden da yawansu ya kai euro miliyan 105, kwatankwacin CFA biliyan 70, domin karfafa samar da ilimi, tsaftar muhalli da kuma kiwon lafiya, yarjejeniyar da suka sanya wa hannu a jiya laraba.
Shugaban tarayyar Jamhuriyar ta Nijar Bazoum Mohammed da kama aiki, ya dau alkawura na kawo gyara ganin kuskuren da aka tafka a bangaren da suka shafi kiwon lafiya,ilimi,tsaro da muhali.
A haka ya kuduri aniyar neman tallafi daga kasashe masu hannu da shuni na ganin sun kawo dfauki ga kasdar ta Nijar.
Daga cikin kasashen da suka jima suna dafawa kasar ta Nijar, kasashen Turai a karkashin kungiyar tarayyar Turai a huldar dake tsakanin su da kasar ta Nijar sun kawo dauki na miliyoyin Euros kamar dai yada wakilinmu Baro Arzika ya aiko mana daga birnin Yameh.
A wani labarin na daban hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana cewar hare haren masu ikrarin jihadi a yammacin Jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar kaurace war dumbin jama’a daga matsugunan su. Hukumar ta kuma jaddada cewar tsanantar kauracewar da jama’ar keyi ya fara ne a cikin watanni biyar na farkon shekara ta 2022 bisa zafafar rashin kwanciyar hankali da ake fuskanta da wasu ke kai hari ga fararen hula da jami’an tsaro ba kakkauta wa.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana cewar an samu matsalolin tsaro har 136 daga watan Janairu zuwa Aprilun wannan shekara sabanin yadda ya kasance sau 93 a shekarar da ta gabata a dai dai irin wannan lokaci.
Daga ranar daya 1 – 19 ga watan mayu an kashe fararen hula 43 tare da awun gaba da wasu 22 a sassan Torodi, Tera da kuma Gotheye a yankin Tillaberib dake da makobtaka da Burkina Faso da Mali a cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumar ta kara da cewa Tun daga farkon watan Afrilun wannan shekara da muke ciki ne dai fiye da mutane dubu 34,700 da ke zaune a Tillaberi matsalar ta tilasta musu ƙaura zuwa wasu wurare da zasu samu natsuwa.
Kasar ta Nijar na fama da matsalar hare haren masu ikrarin jihadi a kan iyakar kasar da Mali da Burkina faso ta yammaci da kuma gabar ta da Najeriya ta Kudanci
Kasar ta Nijar dai ta kasance matsuguni ga dubban wadanda suka kaurace wa matsugunan su tare da yan gudun hijra da suka tsere daga Najeriya, Mali da kuma Burkina Faso.