Tarayyar turai ta bukaci mambobinta da su shirya wa yiwuwar yankewar samar da iskar gas daga Rasha, inda ta zake a kan cewa ba za ta bada kai bori ya hau ba a kan bukatar Rasha ta a biya ta da kudin rubles.
An jiya a yau Talata Tarayyar Turan za ta gabatar da wani sabon kunshin takunkumai da zummar hukunta shugaba Rasha sakamakon mamayar Ukraine da ta yi, ciki har da takunkumi kan sayen danyen manta.
Rasha ta bukaci abokan huldarta daga kasashen da ba sa jituwa, kuma suke sayen gas a hannunta da su biya da kudin ta na rubles, a wani yunkuri na dakushe takunkumin da aka kakaba mata a bangaren hada hadar kudade, kuma a halin da ake ciki, ta katse aikewa da gas kasashen Bulgaria da Poland biyo bayan bijire wa bukatarta.
Tarayyar Turai da Amurka ba su ji dadin mamayar da Rasha ta wa Ukraine ba, lamarin da ya sa suka yi ta kakaba mata takunkumai a bangarori dabam dabam.
A wani labarin na daban Kungiyar agaji ta Red Cross ta nuna damuwa kan yadda Asibitoci a lardin Kivu ta Arewa mai fama da rikici suka cika makel da mutanen da harbi ya jikkata bayan mummunar zanga-zangar adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya da ake ganin ta gaza wajen dakatar da kisan fararen hula a yankin na Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
Tun ranar biyar ga watan nan na Afrelu aka fara gudanar da zanga-zangar da yajin aiki a arewacin Kivi, domin nuna adawa da tawagar Majalisar Dinkin Duniya, sakamakon yadda kungiyoyin masu dauke da makamai ke cikin karensu babu babbaka wajen aikata kisan gilla, zanga-zangar da yayi sanadin mutuwar mutane 10.
Fiye da mutane 120 da suka ji rauni suna jinya a asibitoci a babban biranen Goma da Beni dake arewacin Kivu da taimakon kungiyar agaji ta Red Cross.