Tarayyar Turai EU Ta Sanar Da Dakatar Horar Da Sojojin Kasar Mali.
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yanke shawarar dakatar da ayyukan horas da sojojin Mali, amma za ta ci gaba da kasancewa kasar da ke yankin Sahel.
Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, babban jami’in kula da harkokin waje na EU Josep Borrell ya shaida wa wani taron manema labarai daukar matakin, jim kadan bayan da ya jagoranci taron ministocin harkokin wajen kungiyar da suka tattauna kan batun.
Borrell ya ce abubuwan da ke faruwa a Mali ne suka tilasta musu dakatar da yarjejeniya horas da sojojin kasar, matsalolin da ya ce daga cikinsu akwai katsalandan din da sojojin hay ana Rasha da ke kamfanin Wagner ke yi a kasar ta Mali wadanda aka dorawa alhakin aukuwar wasu munanan al’amura da suka kai ga kashe daruruwan mutane cikin kasar a ‘yan kwanakin nan.
A makon da ya gabata Faransa ta nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa dakarun Mali da sojojin haya na Wagner sun kashe fararen hula sama da 200 a wani samame da suka kai cikin watan jiya a kauyen Moura na yankin tsakiyar kasar.
Rasha dai na cigaba da musanta zargin da ake yi wa sojojinta na aikata ba daidai ba a Mali, wadanda ta ce ta tura su zuwa kasar ne a matsayin masu koyar da ayyukan soji.