Kamfanin dillancin labaran Isra’ila ya rawaito cewa Firaminista Benyamin Netanyahu ya bayar da umarnin sayen tantuna 40,000 daga kasar China da za a kafa a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, a shirye-shiryen kai farmaki ta kasa a Rafah inda Falasdinawa sama da miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Netanyahu ya yi watsi da fargabar da duniya ke da shi na fuskantar bala’in jinƙai idan Isra’ila ta kai farmaki ta kasa a yankin kudancin Gaza, yana mai cewa fararen hula za su iya tserewa fadan zuwa wasu sassan yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Da yake magana da tawagar majalisar dokokin Amurka da ke ziyara a Isra’ila, Netanyahu ya ce mutanen da ke mafaka a Rafah – fiye da rabin al’ummar Gaza miliyan 2.3 – za su iya ficewa daga faɗan.
“Kawai mutane su tafi, su tafi da tantunansu,” in ji Netanyahu a cikin kalamansa na izgilanci. “Mutane sun koma Rafah. Suna iya sake barin can ɗin ma.”
Kutsen da Isra’ila ke shirin yi ya tayar da hankulan duniya saboda birnin, wanda ke kan iyakar Gaza da Masar yana cunkushe da Falasdinawa sama da miliyan 1.5 a sansanoni da tantuna da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wadanda galibinsu suka tsere daga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa wasu wurare.
Kungiyar Musulman Amurka ta yi kira da a gudanar da bincike a Majalisar Dinkin Duniya kan bidiyon da sojojin Isra’ila ke harbewa tare da binne Falasdinawa
Majalisar da ke kula da dangantakar Amurka da Musulunci (CAIR) ta yi kira da a gudanar da bincike na Majalisar Dinkin Duniya kan wani bidiyo da ke nuna sojojin Isra’ila suna harbe wasu Falasdinawa biyu tare da binne su da wata katafila.
“Wannan danyen aikin na yaki da sauran laifuka da makamantansu da gwamnatin Isra’ila mai kisan kiyashi ke aikatawa a kullum, dole ne MDD ta yi bincike a kai a wani bangare na ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi da kawar da wata al’umma da azabar yunwa da ake gana wa al’ummar Falasdinu tare da hadin gwiwar gwamnatin Biden,” in ji Daraktan Sadarwa na CAIR Ibrahim Hooper a wata sanarwa da ya fitar.
DUBA NAN: Jihohin Arewa Sun Ware Kudi Domin Ciyarwa A Watan Azumi
Ya ƙara da cewa “Dakarun gwamnatin Isra’ila masu tsattsauran ra’ayi da alama suna kashe Falasdinawa ne da son rai, sannan kuma suna daukar gawarwakinsu tamkar bola, dole ne a dakatar da wannan kisan kiyashi, ba wai ba da uzuri ko tallafa musu da makamai da maganganu ba.”