A cikin wani bayani da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi ga mayakan kungiyar a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki a kasar, kuma sun shimfida ikonsu a jihar Panjshir wadda taki mika wuya.
Baya ga haka kuma kungiyar ta nuna hotunan bidiyo na babban ginin gwamnatin jihar Panjshir, inda mayakan kungiyar suka saukar da tutar kasar Afghanistan da ke wurin, suka dora tutarsu.
Sai dai a nasa bangaren Ahmad Mas’ud wanda ke jagorantar mayakan yankin na Panjshir wajen yin turjiya a gaban mayakan Taliban tare da kin mika wuya gare su ya karyata cewa Taliban ta kammala kwace iko da jihar baki daya.
Haka nan kuma ya yi ikirarin cewa, sunan nan cikin jihar kuma za su gaba da yaki da Taliban, kamar yadda ya bukaci al’ummar Afghanistan da su mike su kwaci ‘yancin kansu daga mulkin mallakar Taliban.
A wani labarin na daban babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana bukatar yin aiki da Iran domin tabbatar zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai daurewa a fadin duniya.
A wata wasika da ya aike wa shugaban kasar ta Iran Ibrahim Ra’isi, babban sakataren na MDD, ya taya zababben shugaban kasar ta Iran murna akan zabin da akayi masa, tare da fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnatin ta Iran.
Guterres ya kara da cewa, ’shugabancin ka ya zo a daidai wani lokaci mai tsanani a fadin duniya, inda ake fama da annobar korona, canjin yanayi da rikice rikice suka mamaye duniya ciki har da a yankin gabas ta tsakiya’’.
Saboda haka babban sakataren na MDD, ya bayyana fatansa ga shugaban kasar ta Iran, na yin aiki tare, domin cimma burin da aka sanya a gaba na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai daurewa da kare hakkin dan adam a duniya baki daya.