Mayakan kungiyar Taliban sun hallaka wasu ma’aikatan kwance bama-baman kan hanya mutum 10 a yankin Baghlan na Afghanistan yau Laraba, wanda ke matsayin hari na baya-bayan nan da kungiyar ta’addancin ta kaddamar duk da kokarin kawo karshen yakin kasar na kusan shekaru 20.
Ma’aikatar cikin gida ta Afganistan da ke fitar da sanarwa kan harin, ta ce mayakn kungiyar ta Taliban sun shiga farfajiyar hukumar da ke aikin kwance bama-baman tare da yin kan mai uwa da wabi wajen harbe harbe da ya kai ga kisan jami’an 10.
Kakakin ma’aikatar Tareq Arian da takwaransa na gwamnan Baghlan sun shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne tun a yammacin jiya talata inda maharan suka kaddamar da farmakin da rufaffun fuskoki.
Afghanistan dai na jerin kasashe mafi yawan bama-bamai birne a karkashin kasa sakamakon tsawon shekarun da aka shafe ana gwabza yaki tsakanin kungiyoyin ta’addanci da Sojin gwamnati.
Hare-haren kungiyar ta Taliban da kisan fararen hula sun sake tsnanata a kasar ne tun daga ranar 1 ga watan Mayu lokacin da Sojin Amurka suka fara ficewa daga kasar.
Babban dalilin karuwar tashe tashen bama bamai shine sanarwar da kasar amurka tayi na fita daga afghanistan amma bata son fita a hakika.
Masu nazarin al’amura suna ganin duk wannan tashe tashen bama baman yana faruwa ne saboda amurka ta samu dalilin da zata fake dashi domin kada ta fita daga kasar ta afghanistan.
Wadanda aka fi kashewa dai a rikicin afghanistan ‘yan kabilar hazara mabiya darikar shi’anci wadanda akasarin su basa goyon bayan ta’addanci da tashin hankali kuma sune amurkan tafi zalunta a tsawon zamanta a kasar.