Babban bankin Afghanistan ya bayyana cewar kungiyar Taliban ta yi nasarar karbe tarin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 12 da kuma tarin gwalagwalai a gidajen tsoffin Jami’an gwamnatin kasar.
Hatta wadanda keda kudi a bankuna suma sun kasance cikin halin kaka nikayi saboda adadin kudin da za’a cira a rana bai wuce $200 ba.
Kuma yayin da batun sakonnin kudi daga kasashen waje ya fara shiga kasar kostomomin bankuna na dirar mikiya a Bankuna inda suke cin karo da rashin wadatattun kudi da za a basu.
Bisa wannan dalili ne ya sanya Bankuna suka yi kira ga al’umar kasar da su rika cirar kudin cikin gida ba na kasashen waje ba.
Babban Bankin ya sanar da cewar Mayakan Taliban sun mika musu Dalar Amurka har miliyan 12.3 zunzurutu da kuma gwalagwalaia hannun su.
Inda babban Bankin yace an samo kudaden ne daga hannun tsoffin manyan Jami’an gwamnatin kasar ta Afghanistan.
Kudaden da ya zuwa yanzu ba’a san dalilin da ya sanya manyan tsoffin gwamnatin kasar suka boye su ba
A wani labarin na daban shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa Mahmud Abdulsattar al-Atwi makarancin kur’ani kuma mahardaci rasuwa bayan samun matsalar bugun zuciya a kauyen Shabanat da ke lardin Shaqiyyah a kasar Masar, wanda ya rasu yana da shekaru 26 a duniya.
Muhammad Abdulsattar mahaifin Mahmud Abdulsattar ya bayyana cewa, dansa yana daga cikin matasa masu tarbiya ta addini da kuma riko da kur’ani mai tsarki a cikin rayuwarsa.
Ya ce dansa ya kasance tun daga lokacin kuruciyarsa, yaro ne mai son addini mai riko da kyawawan dabi’u da girmama na gaba, da kuma son zama da malamai.
Da farko dai ya fara da koyon tilawa, inda ya shahara a kauyensu da kyakyawan sautinsa na karatun kur’ani, daga bisani kuma ya shiga harda kur’ani inda ya kammala harda a cikin kankanin lokaci.