Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, dakin karatu na birnin Iskandariyya a kasar Masar na ajiye da takardun tafsirin kur’ani mafi jimawa a duniya, wanda ake kira da tafsirin Albusti, wanda Abu Ishaq Bin Ibrahim Albusti ya rubuta shi, wanda ya rasu shekara ta 307 bayan hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina.
Tun daga wancan lokaci wannan tafsiri ake kula da shi shekaru bayan shekaru, wanda daga karshe dai ya isa dakin karatu na birnin Iskandariyya, wada yake dauke da littafai masu tarin yawa da aka rubuta su shekaru masu yawa da suka gabata a cikin takardu da fatunsu na asali.
Baya ga tafsirin ayoyin kur’ani, akwai hadisan ma’aiki a cikin takardun littafin, wadanda suke bayani kan ayoyi da kuma bayanin saukarsu.
Sannan kuma an rubuta a cikin shafuka 233, kuma a cikin shafi akwai shedara 21 da tsarin rubutu da ake kira magribi.
Nadiya Al-sharif ita ce shugabar bangaren baje koli na babban dakin karatu na birnin Iskandariya, ta bayyana cewa akwai dadaddun littafai da takardun makamantan wannan da yawansu ya kai 120 a cikin wannan dakin karatu da ake adana su.
A wani labarin na daban shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi Amru Laisi ya gana da babban malamin Azhar Sheikh Ahmad Tayyib a ofishinsa da ke birnin Alkahira.
A yayin wannan ganawa bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi da kuma ayyukan da suke gudanarwa na wayar da kan al’umma.
Babban malamin na Azhar da kuma shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi sun cimma matsaya kan gudanar da taro na kasa da kasa na gidajen rediyon kasashen kasashen musulmi, musamamn na kur’ani.
Babbar manufar taron dai ita ce kara fayyace muhimman ayyuka da suka shafi sadarwa a kasashen musulmi, inda masana za su gabar da bayanai kan hakan
Baya ga haka kuma sun cimma matsaya kan bayar da horo na musamman dangane da ayyukan kafofin yada labarai an musulmi, wanda cibiyar Azhar za ta dauki nauyinsa.
An kafa cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi zaman taron karo na 6 na kungiyar kasashen musulmi ta OIC a shekara ta 1975, kuma wannan cibiya tana karkashin kungiyar kasashen musulmi ne.