A ranar laraba ne shugabar majalisar Amurka Nanci Pelosi ta bar Taiwan a wata ziyarar bazata wacce ta girgiza duniya kuma ta sanya tsoron barkewar sabon yaki a yankin asiya, bayan wanda duniya ke fama da shi tsakanin Rasha da Ukraine.
Ziyarar ta pelosi dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake tsaka da tataburza dangane da yankin taiwan wanda wani bangare ne mai muhimmanci na kasar chaina.
Kasar chaina dai ta nuna matukar rashin goyon bayan ta ga wannan ziyara wacce ta bayyana a matsayin keta hurumin iyakokin ta.
Ko shugaban kasar Amurka Joe Biden ma a gabanin tafiyar ta Pelosi ya bayyana rashin hikima a wannan tafiya da tsohuwar zatayi zuwa yankin asiya.
Duk da matsalolin lafiya gami da tsufa, sakamakon zargin kamuwa da cutar korona da ake ma Nanci Pelosi amma sai da aiwatar da wannan tafiya, lamarin daya kara tsamama haklin dar dar din da ake ciki a yankin asiya.
Kuma wannan lamari ya sanya kasar chaina wacce ke da karfn soji ta sha alwashin hukunta duk wadanda ke da hannu a kitsa wannan ziyarar karya doka ta Pelosi din.
Chainan ta bayyana wannan lamari a matsayin keta alfarmar iyakokin chaina da Amurka tayi da sunan dimokoradiyya kuma ta lashin takobin hukunta masu hannu a wannan lamari.
A bayan ziyarar dai chaina tace, a matakin farko ya zama dole ta kaddamar da atisayen ba sani ba sabo a gewayen Taiwan din domin tabbatar da lamurra suna cikin tsari gami kuma da tauna tsakuwa domin aya taji tsoro.
Ziyarar ta Pelosi dai ba baya da kura kurum ta bari a yankin gabas ta tsakiya ba, ta kuma bude kofar tofa albarkacn bakin masu amfani da kafafan sada zumunta, inda wasu ke ganin ziyarar a matsayin tsokana wanda hakan bai dace ba musamman duna da yakin Rasha da Ukraine na tsaka da wakana bai kamata a takalo wani rikicin ba.
Wasu kuma na ganin idan Chaina, Rasha da kuma Iran suka hade kai zasu iya kai amurka kasa