A jiya asabar ne , Shugaban kasar China, Xi Jimping ya yi bikin tuni da zagayowar ranar juyin juya hali ,shekaru 110 da suka gabata ya dau daukar alkawalin sake hada tsibirin Taiwan da kasar ta China.
Tsai Ing –Wen Shugabar Taiwan wacce ta mayar da martani ga China,ta na mai cewa har idan ta kama ,Taiwan za ta kare kan ta da ci gaba da kasancewa a karkashin tsarin demokurradiyya.
Taiwan dake da yawan al’uma da suka kai milyan 23 na rayuwa ne cikin barazanar China da kan iya mamaye ta a duk lokacin da ta ga dama.
Shugabar a karshe ta na mai cewa ,fatan kowace kasa shine na kasancewa cikin zaman lafiya da makwabta.
A wani labarin na daban kungiyar Taliban ta gargadi Amurka da ta kaucewa yiwa sabuwar gwamnatin Afghanistan zagon kasa yayin wani taron gaba da gaba da wakilan bangarorin biyu suka gudanar a Doha.
Muttaqi yace dangantaka mai kyau da gwamnatin Taliban zai taimaki kowanne bangare, saboda haka babu dalilin yiwa sabbin jagororin zagon kasa domin jefa kasar cikin tashin hankali.
Jawabin ministan harkokin wajen na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara taron kwanaki biyu tsakanin wakilan kasashen biyu, wanda ya samu halartar Mataimakin Jakada na musamman na Amurka Tom West da kuma babbar jami’ar Hukumar Jinkai ta USAID Sarah Charles.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace babu wani martani da ya samu daga bangaren Amurka dangane da wadannan kalamai.
A watan Agustan da ya gabata ne kungiyar Taliban ta karbe iko da kasar abinda ya kawo karshen shekaru 20 da dakarun Amurka suka mamaye Afghanistan.