Hukumomin Kasar Sweden sun tasa keyar wani dan kasar Rwanda zuwa gida domin amsa tuhuma dangane da zargin da ake masa na hannu a kisan kare dangin da aka yi a kasar.
An kama Micomyiza mai shekaru 50 a Sweden ne a watan Nuwambar shekarar 2020 sakamakon sammacin haka da Rwanda ta gabatar, yayin da akayi ta shari’a akan halarcin tasa keyar sa gida domin fuskantar tuhumar ko kuma akasin haka.
Ana tuhumar sa ne da hannu wajen neman Yan kabilar Tutsi inda suke nuna su domin hallaka su a shekarar 1994 lokacin yana matashi mai shekaru 22.
A wani labarin na daban Mali ta zargi sojojin Faransa da yi mata leken asiri a lokacin da suka yi amfani da wani jirgi mara matuki wajen daukar hoton abin da Faransa ke zargin sojojin haya ne ke binne gawarwaki a kusa da wani sansanin soji.
Kwana daya da faruwar hakan, sojojin Faransa sun watsa wani faifan bidiyo da ta ce ya nuna sojojin hayar Rasha suna rufe gawarwaki don zargin sojojin Faransa da suka fice da aikata laifin.
Da sanyin safiyar Talatar nan ne dai rundunar sojojin Mali ta sanar da gudanar da bincike kan gano wani kabari da aka yi a sansanin na Gossi.
Rundunar ta ce ta gano kabarin ne washegarin da aka wallafa hotunan.
Mali dai ta zargi Faransa da yin leken asiri da kuma yunkurin bata sunan sojojin ta da bidiyon da aka dauka da jirgi mara matuki.
Kakakin gwamnatin kasar Abdoulaye Maiga ya ce, anyi amfani da jirgin maras matuki ne domin yin leken asiri ga dakarun sojin Mali.